Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Zai Ƙaddamar Da Gangamin Yaƙin Neman Zaben Sa A Kaduna

* Zai Karaɗe Ƙasar Nan Gabanin Zaben 2027 Darakta-Janar na Kwamitin Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Sanata Abdula...



* Zai Karaɗe Ƙasar Nan Gabanin Zaben 2027

Darakta-Janar na Kwamitin Gangamin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da jadawalin ziyartar jihohin ƙasar nan gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Sanata Yari ya ce za a fara gangamin zaɓen APC a ranar 24 ga Oktoba a Kaduna, yayin da aka tsara gudanar da taron farko na kwamitin gangamin a ranar 14 ga Oktoba a zauren taro na Banquet Hall da ke Fadar Shugaban Ƙasa.

Yari ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ya ƙara da cewa bayan ƙaddamar da kwamitin, gangamin wayar da kan jama’a da neman goyon baya zai ci gaba zuwa Fatakwal da ke Jihar Rivers, da kuma Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Sai dai ya ce za a fitar da cikakken jadawalin ziyarar jihohin ne bayan ƙaddamar da kwamitin gangamin.

A yayin ganawar, Sanata Yari ya kuma yi magana kan 'yan takarar adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Ya bayyana cewa 'yan siyasar ba su da isasshen goyon baya a Arewa da Kudancin Nijeriya da zai ba su damar samun nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.

A cewarsa, Shugaba Tinubu na da gagarumin goyon baya a jihohi fiye da goma a kowane yanki na Arewa da Kudu, yana mai cewa APC za ta dogara da nasarorin da gwamnatin ta samu wajen gabatar da manufofinta ga masu zaɓe.

Sanata Yari ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta inganta yanayin tattalin arzikin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, yana mai cewa jam’iyyar za ta gabatar da nasarorin gwamnatin a matsayin hujjojin neman wa’adin mulki na biyu.

No comments