Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Abba Kabir Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Nafiu Baba Ahmed

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhinin sa da kaɗuwa kan rasuwar Malam Nafiu Bab...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhinin sa da kaɗuwa kan rasuwar Malam Nafiu Baba-Ahmed, Sakatare Janar na Majalisar Ƙoli ta Shari'ah a Nijeriya .

A cikin saƙon ta'aziyya da Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata 6 ga Oktoba, 2026, Gwamna Yusuf ya bayyana rasuwar ta a matsayin babban rashi ga Al'ummar Musulmi, kasa baki ɗaya.

Gwamna Yusuf ya ce Nijeriya ta yi babban rashi na fitaccen Lauya, ƙwararre a harkar kuɗi, mai kare harkokin Musulunci kuma haziƙin masanin harkokin jama'a wanda ya sadaukar da shekaru masu yawa na rayuwar sa wajen inganta adalci, kyakkyawan shugabanci da fahimtar addini.

Gwamnan ya yaba da irin jajircewar sa da shugabanci nagari da ya bayar a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Shari'ah, inda ya kasance murya mai ƙarfi kan al'amuran da suka shafi Musulunci, haƙƙin da kundin tsarin mulki ya bayar, adalci da ci gaban ƙasa.

Haka kuma, Gwamna Yusuf ya yaba wa marigayin kan irin gagarumar gudumawar da ya bayar a fannin shari'a da harkokin kuɗi, ciki har da aikin sa a Hukumar Inshorar Ajiya ta Nijeriya (NDIC) da kuma gudumawar da ya bayar wajen bunƙasa harkar Musulunci a Nijeriya.

Ya ce za a tuna marigayin da jarumtakarsa, zurfin iliminsa, tawali'unsa da jajircewarsa wajen tabbatar da adalci da hidima ga al'umma.

A madadin Gwamnati da al'ummar Jihar Kano, Gwamna Yusuf ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan Malam Nafiu Baba-Ahmed, shugabanci da mambobin Majalisar Shari'ah ta Ƙasa, al'ummar Jihar Kaduna da ɗaukacin al'ummar Musulmi.

Ya roƙi Allah (SWT) da ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da ayyukansa na alkhairi, ya ba shi Aljannatul Firdausi, tare da ba wa iyalansa haƙuri da karfin jure wannan babban rashi.
 

No comments