Daga Hussaini Yero, Gusau Darakta mai kula da harkokin Matasa na Ɗan takarar Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wato ATIKU PULSE, Hon Lawali Is...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Darakta mai kula da harkokin Matasa na Ɗan takarar Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wato ATIKU PULSE, Hon Lawali Isah Gusau, mazaunin Kaduna ya bayyana cewa takurawa da matsin Lamba da ake yi wa 'yan Jam'iyyar adawa ta ADC A Kaduna ne ya jawo mata farin jini, don yanzu haka sama da ƙungiyoyi 2000 suka bar APC mai mulkin Jihar Kaduna suka dawo ADC.
Hon. Lawali Isah ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau cikin makon nan.
Daga nan Lawali Isah ya bayyana takaicinsa na ganin yadda Jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kaduna ke takurawa Jam'iyyun adawa, musamman 'yan takarar Jam'iyyar ADC, wanda hakan ba zai haifar wa Jam'iyyar APC mai mulkin ɗa mai ido ba.
Don haka Daraktan ya yi kira ga jigajigan Jam'iyyar APC da su tuna a zaben 2023, abin da ya faru A Zamfara, yadda Ake ma Jam'iyyar ADC zagon ƙasa da takura masu ta kowane bangare, haka aka yi wa Jam'iyyar PDP A Zamfara, amma cikin ikon Allah sai ga shi Gwamna Matawalle, duk da yake suna da gwamnati a sama da ƙasa, sai ga shi wanda bai taba yin ko Kansila ba, ya lashe zaben Gwamna kuma har da 'yan Majalisu Jiha da na tarayya.
"Akan haka nake kira ga 'yan Jam'iyyar APC mai mulkin a Kaduna ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Uba Sani da su yi taka-tsantsan akan takura wa Jam'iyyun adawa, idan kuwa ba haka ba, to za su sha mamaki," inji Lawali Isah.
Da ya koma kan 'Yan Arewa kuwa, Daraktan ya yi waiwaye, inda ya kawo misalin ganawar Hajiya Naja'atu a ƙasar Landan da Bola Ahmad Tunubu, lokacin yan takara a 2023, inda ya bayyana mata cewa babu wani shiri da ya yi akan batun Arewa, sai dai idan ya ci zabe zai ga abin da zai yi masu.
Wannan ne ya sa Hajiya Naja'atu ta ƙi mara masa baya, kuma ta bayyana Dalilanta ƙarara kowa ya ji, amma duk da haka wasu su 'Yan Arewan suka zabi Jam'iyyar APC da Bala Ahmad Tunubu a zaben Shugaban ƙasar, yanzu ga inda ya kai mu nan.
Don haka ne Darakata Lawali Isah yake kira ga al'ummar Arewa da su yi Karatun ta-natsu akan zabe mai zuwa na 2027 don kada su bi son zuciyar su, ko wasu 'Yan barandan Shugaban ƙasa su yaudare su da wani abu ɗon su zabi Jam'iyyar APC.
Lawali Isah ya kuma tabbatar da cewa, idan al'ummar ƙasar nan suka zabi Jam'iyyar ADC, wacce Atiku Abubakar ke ma Takarar Shugaban ƙasa, da kuma dukkan 'yan takar su, to lallai matsalar ta'addanci ƙasar nan ta zo ƙarshen da yardar Allah.

No comments