Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

JIHAR FILATO: Yadda Mata Suka Riƙi Ragamar Kasuwanci A Wasu Kasuwanni

Daga Idris Ibrahim Azare Kusan dukkan kasuwannin garuruwan Bokkos, Mangu da Barikin Ladi da ke wajen birnin Jos, a Jihar Filato, mata ne suk...


Daga Idris Ibrahim Azare

Kusan dukkan kasuwannin garuruwan Bokkos, Mangu da Barikin Ladi da ke wajen birnin Jos, a Jihar Filato, mata ne suka mamaye harkokin kasuwanci, inda suke taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da tattalin arziƙin yankin.

Kasuwannin dankalin Turawa, dankalin Hausa, kabeji, rake, masara, kayan miya da sauran kayan amfanin gona na daga cikin kasuwannin da mata ke gudanar da harkokinsu na saye da sayarwa.

A mafi yawan lokuta, idan ka shiga waɗannan kasuwanni, mata ne za ka tarar suna hada-hadar kasuwanci, yayin da mazaje da ka gani sukan kasance masu sayayya ko kuma waɗanda suka zo domin karɓar kuɗi daga matansu.

Wannan yanayi ya sa ake kallon matan yankin a matsayin waɗanda suka riƙe ragamar kasuwanci da tattalin arzikin iyalansu. Wasu daga cikinsu suna gudanar da harkokin kasuwanci ne domin ciyar da iyalansu, biyan buƙatun gida da kuma tabbatar da cewa ’ya’yansu sun samu ilimin da zai taimaka musu a rayuwa.

Wani abin lura shi ne yadda ake samun sabani wajen amfani da kalmar “ci-ma-zaune” a tsakanin maza da mata. A wasu lokuta, maza kan yi amfani da wannan kalma wajen sukar matan da ba sa gudanar da ayyukan da suke ganin ya kamata su yi, haka kuma mata kan yi amfani da ita wajen bayyana rashin gamsuwarsu da mazajen da ba sa bayar da gudummawa wajen tafiyar da iyali.

Sai dai abin da ya cancanci a yi nazari a kai shi ne yadda mata a waɗannan yankuna ke iya ɗaukar nauyin kasuwanci, kula da gida da kuma tallafa wa karatun ’ya’yansu har zuwa matakin jami’a, duk da irin ƙalubalen da suke fuskanta.

Tambayar da ta kamata mu yi ita ce: Shin ya dace a kira mace “ci-ma+zaune” saboda ba ta fita kasuwanci, alhali kuwa akwai mazajen da ba sa gudanar da kasuwanci, amma matansu ne ke ɗaukar nauyin iyalansu? Haka kuma, idan mace tana iya ɗaukar nauyin iyali, kula da yara da kuma tallafa wa karatunsu, me ya hana a yaba mata bisa wannan ƙoƙari?

A ƙarshe, ya kamata mu fahimci cewa gina iyali da bunƙasa tattalin arziki ba nauyin jinsi guda ba ne. Miji da mata suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban iyali da kuma makomar ’ya’yansu.

 

No comments