Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Bindiga Sun Kashe Magidanci, Sun Sace Matarsa Da ’Ya’yansa A Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun kashe wani magidanci tare da yin awon gaba da matarsa, ’ya’yansa biyu da wasu mutane shida a wani hari da suka kai ung...




Wasu ’yan bindiga sun kashe wani magidanci tare da yin awon gaba da matarsa, ’ya’yansa biyu da wasu mutane shida a wani hari da suka kai unguwar Babban Saura da ke ƙaramar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

An ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Alhamis, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici, bayan ’yan bindigar sun kutsa cikin gidaje uku tare da yin awon gaba da wasu daga cikin mutanen da ke cikinsu.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun fara shiga gidan wani dattijo, inda suka yi awon gaba da ’ya’yansa biyu, kafin daga bisani su nufi gidan wani mazaunin yankin da aka bayyana da sunan Sikiru.

A cewar majiyar, ’yan bindigar sun haura katangar gidan Sikiru suka shiga harabar gidan, kafin su nufi ɗakin tarbar baƙi, inda ake zargin suka kashe shi.

Daga nan ne suka yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa biyu.

Har ila yau, maharan sun shiga wani gidan da ke makwabtaka da gidan mamacin, inda suka sace wata mata tare da ’ya’yanta huɗu. Sai dai daga bisani sojoji tare da ’yan sa-kai suka yi nasarar ceto matar, yayin da ’ya’yanta huɗu suka ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindigar.

An tattaro cewa Sikiru ya yi ƙoƙarin hana maharan shiga ɗakin tarbar baƙin gidansa, inda ya yi gumurzu da wasu daga cikinsu kafin daga bisani su kashe shi.

Kwamandan ’yan sa-kan yankin, Usman Adamu, wanda ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, ya ce jimillar mutane tara aka yi awon gaba da su a farkon harin.

Adamu ya ce ’yan sa-kan sun samu kiran neman ɗauki cewa ’yan bindiga sun mamaye yankin, nan take suka sanar da sojoji, waɗanda suka haɗa kai da su wajen bin sawun maharan.

“Mun samu kiran neman ɗauki cewa ’yan bindiga sun shiga Babban Saura PW, sai muka sanar da sojoji suka haɗa kai da mu. Mun bi sawunsu har zuwa yankin Eastern Bypass, inda muka yi nasarar ceto wata mata mai suna Maman Mubarak, wadda ’ya’yanta huɗu na cikin mutanen da aka sace,” in ji shi.

Kwamandan ya ƙara da cewa sojojin sun yi ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, amma maharan sun tsere tare da su.

Wani maƙwabcin mamacin da ya bayyana sunansa da Anas ya ce Sikiru ya kira shi ta waya bayan ’yan bindigar sun mamaye yankin.

A lokacin da wakilin Daily Trust ya ziyarci garin, an tarar da ’yan uwa da abokan arziki da sauran masu juyayin rasuwar sun taru a gidan mamacin, suna nuna damuwarsu kan mummunan harin.

Harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wasu ’yan bindiga da ake zargi da aikata laifuka suka kai hari ƙauyen Kadaure, wanda ba shi da nisa da Babban Saura, inda suka kashe wani mutum tare da awon gaba da shanunsa.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, kan harin, amma ba a samu damar magana da shi ba, saboda wayarsa ba ta shiga. Haka kuma, har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, bai mayar da martani ga saƙon tes da aka aika masa ba.

No comments