Daga Hussaini Yero, Gusau A yayin da Jihar Zamfara bikin cika shekara 30 da samuwa, an bayyana waɗannan da cewa al'ummar jihar sun amfa...
A yayin da Jihar Zamfara bikin cika shekara 30 da samuwa, an bayyana waɗannan da cewa al'ummar jihar sun amfana da ayyukan more rayuwa ta kowane bangare.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Nakwada ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a Ofishin sa da ke Sakatariyar Jabril Bala Yakubu da ke Gusau.
Nakwada ya bayyana cewa,tarihin shekaru 30 da samuwar jihar Zamfara abun godiya ne ga Allah da kuma murna ga al'umma, Sarakunan gargajiya, ma'aikatan gwamnati da 'yan ƙasa waɗanda suka bayar da gudumawa ga ci gaban Zamfara tun lokacin da aka ƙirƙiro ta a 1996.
Sakataren gwamnatin ya ce, "Muna godiya ga waɗanda suka bada gudumawa tare da girmamawa da sadaukarwar da suka yi na samuwar Jiharmu ta Zamfara.
"A lokaci guda, wannan bikin cika shekaru yana nazari kan sauyin da aka samu a cikin shekaru uku da suka gabata ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal, Gwamnan Jihar Zamfara, da kuma shiga sabon babi a tafiyar ci gaban mu na shekaru 30.
"Tun daga Mayu 2023, gwamnatin ta samu ci gaba a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, noma da baben more rayuwa, ci gaban ɗan adam, gyaran cibiyoyi da ci gaban tattalin arziki".
"Gwamnatin ta tabbatar da cewa ba za a iya samun sauyi mai ma'ana da ɗorewa ba tare da tsaro ba".
" A Jihar da ta sha fama da harin 'yan bindiga, garkuwa da mutane da tarwatsa rayuwar mutanen karkara, dawo da tsaro ya zama ginshiƙi wajen sake gina al'ummomi, da dawo da su garuruwan su ,su ci gaba da Noma don shi ne ginshiƙin tattalin arzikin su.
Daga nan Nakwada ya tabbatar da cewa, Gwamnatin Jihar ta ci gaba da bayar da gagarumin goyon baya ga Rundunar Sojoji, Rundunar 'Yan Sanda ta Nijeriya, Hukumar Tsaro na Farin Kaya (DSS), Hukumar Tsaron Farar Hula da sauran hukumomin tsaro na yau da kullum da ke aiki a Zamfara.
Kuma mun samar da motocin aiki, motocin yaƙi masu sulke, jiragen sama marasa matuki na leƙen asiri (drones), babura na musamman da sauran kayan aiki na dabaru da aiki domin ƙarfafa motsi, sa ido, tattara bayanan sirri da kuma gaggauta kai dauki.
A matakin jiha Gwamnati ta kafa Ƙungiyar Tsaron Al'umma (Community Protection Guards - CPG) a matsayin ƙungiyar tsaro mai goyon bayan Jihar domin tallafawa hukumomin tsaro na yau da kullum, musamman ta fuskar bayanan sirri dan dakile 'yan bindiga da suka addabemu.

No comments