Daga IdrisIbrahim, Azare An gudanar da wani gagarumin shiri na rabon kayan ɗaki da sauran kayayyakin tallafin aure ga marayu da masu ƙaramin...
Daga IdrisIbrahim, Azare
An gudanar da wani gagarumin shiri na rabon kayan ɗaki da sauran kayayyakin tallafin aure ga marayu da masu ƙaramin ƙarfi a garin Azare ta Ƙaramar Hukumar Katagum da ke Jihar Bauchi, domin taimaka musu wajen shirye-shiryen aure da kuma rage musu nauyin da ke tattare da kafa iyali.
Shirin, wanda ya shafi mutane 40, an gudanar da shi ne a Garage na Ƙaramar Hukumar Katagum da ke Azare, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar Katagum, Hon. Yusuf Babayo Zaki, Kauran Azare.
A yayin taron, Hon. Sunusi Talba Media ne ya jagoranci ƙaddamar da kayayyakin tallafin, a madadin shugaban Ƙaramar Hukumar, waɗanda aka tanada domin kai agaji ga marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ke fuskantar ƙalubale wajen shirya abubuwan da suka dace da fara rayuwar aure.
Bayan ƙaddamar da kayayyakin, an miƙa su ga ƙungiyoyi irin su Aytam Global Charity da sauran ƙungiyoyin da abin ya shafa, domin su tabbatar da raba tallafin ga mutanen da aka tsara shirin domin su.
Tallafin ya ƙunshi kayan ɗaki da sauran kayayyakin da za su taimaka wa waɗanda suka amfana wajen fara rayuwar aurensu, musamman ganin yadda shirye-shiryen aure ke buƙatar kuɗaɗe da dama, abin da kan zama babban ƙalubale ga marayu da masu ƙaramin ƙarfi.
Masu shirya shirin sun bayyana cewa manufar tallafin ita ce rage wa waɗanda suka amfana wasu daga cikin nauyin da ke kansu, tare da ba su damar fara rayuwar iyali cikin sauƙi da mutunci.
Shirin ya kuma kasance wani muhimmin mataki na nuna yadda haɗin kan al'umma da tallafawa masu buƙata zai iya taimakawa wajen sauƙaƙa rayuwar jama'a, musamman marayu da waɗanda ba su da isasshen ƙarfin tattalin arziki.
A cewar masu ruwa da tsaki, taimakon marayu da masu ƙaramin ƙarfi ba wai kawai taimakon mutum ɗaya ba ne, a'a, hanya ce ta gina al'umma mai tausayi da haɗin kai, inda waɗanda suke da hali ke tallafa wa waɗanda ke buƙata.
Rabon kayan ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara jaddada muhimmancin tallafawa matasa da masu shirin kafa iyali, domin rage musu matsalolin da kan iya kawo cikas ga shirye-shiryen aurensu.
A ƙarshe, shirin ya ƙara fito da muhimmancin haɗin gwiwar hukumomi da ƙungiyoyin jin ƙai wajen tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi, tare da ƙarfafa al'umma da ta ci gaba da bai wa irin waɗannan mutane kulawa da tallafi.
Mutane 40 ne suka samu damar amfana da wannan tallafi, wanda aka yi shi da nufin sauƙaƙa musu wajen kafa iyalansu da fara sabuwar rayuwa.
Wasu da suka amfana da wannan tallafi, waɗanda wakilin mu ya tattauna da su sun nuna matuƙar jin dadin su da wannan tagomashi.






No comments