Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta gano inda ake zargin ana tsare da ’yan Nijeriya 19 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa sansanonin horas da ...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta gano inda ake zargin ana tsare da ’yan Nijeriya 19 da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa sansanonin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima, amma jami’an tsaro sun jinkirta kutsawa sansanin saboda fargabar cewa ’yan bindigar sun dasa bama-bamai a wurin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo, Audu Garba Bosso, ne ya bayyana hakan ranar Asabar yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya bayar da sabon bayani kan aikin ceto mutanen da aka sace.
Bosso ya ce jami’an tsaro sun yi amfani da jirage marasa matuƙa (drones) ranar Juma’a wajen gano sansanin da ake zargin masu garkuwar suke amfani da shi, bayan jami’an tsaro sun bi sawun maharan har zuwa cikin daji.
Sai dai ya ce jami’an tsaron sun yi taka-tsantsan wajen kai farmaki saboda bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa an tanadi bama-bamai ƙirar hannu, wato IED a sansanin.
“Ko a wane lokaci za mu shiga dajin. Jiya mun shiga dajin, mun bi sawunsu har muka kai wani wuri.
“Amma a wannan lokacin ba mu iya kutsawa zuwa inda bayanan wurin da jirgin mara matuƙin ya nuna mana suke ba, domin mun yi amfani da drones jiya, kuma sun nuna mana ainihin inda suke.
“Amma matsalar da muke fuskanta ita ce, bisa bayanan sirrin da muka samu, an cika sansanin da IEDs,” in ji kwamishinan.
Bosso ya ce hukumomin tsaro suna shirin kutsawa yankin da manyan kayan aiki, ciki har da bulldozers da motocin ɗaukar jami’an tsaro masu sulke (APCs), domin ceto mutanen cikin aminci ba tare da sun samu rauni ba.
Ya ce: “Muna shirin shiga wurin da manyan motocin aiki, wato bulldozers, tare da APCs, domin mu ga yadda za mu ceto waɗannan mutane ba tare da sun samu rauni ba.”
Yadda aka sace ’yan NYSC 19
Wannan sabon bayani ya zo ne kwanaki biyu bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 19 da ke shirin fara aikin yi wa ƙasa hidima, waɗanda suke tafiya daga Ibadan ta Jihar Oyo zuwa sansanonin horas da NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.
An kai harin ne ranar Alhamis a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha, a yankin Umunoha da ke Jihar Imo.
Waɗanda aka sace suna cikin motocin bas guda biyu ne lokacin da maharan suka tare su tare da tilasta musu shiga cikin daji.
Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Uko Akwa Ibom Motors Nigeria Limited, Isiah Akpan, ya shaida wa Saturday PUNCH cewa maharan sun tafi da fasinjoji 19, waɗanda dukkansu ’yan NYSC ne da ke shirin fara aikin yi wa ƙasa hidima.
Ya ce direbobin motocin sun tsere ne bayan harin, sannan suka sanar da jami’an tsaro da ke wani shingen bincike da ke kusa, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka fara binciken yankin domin gano waɗanda aka sace.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun nemi a biya su Naira miliyan 50 kan kowane mutum, wanda ke nufin jimillar kuɗin fansar mutanen 19 ta kai Naira miliyan 950.
An kuma tuntubi wasu iyalan waɗanda aka sace ta wayoyin ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su.
Daya daga cikin iyayen waɗanda abin ya shafa, Misis Oladosu, ta shaida wa Saturday PUNCH cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalinsu ta wayar ɗiyarta, inda har suka ga wasu daga cikin waɗanda aka sace yayin wata tattaunawa ta bidiyo.
Tun da farko, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta sanar da cewa an ceto mutane 10. Sai dai Kakakin Rundunar, Henry Okoye, bai iya tabbatar da ko waɗanda aka ceto suna cikin ’yan NYSC 19 da aka sace ba.
Rundunar ta kuma ce jami’an tsaro sun ci gaba da gudanar da aikin bincike da ceto cikin haɗin gwiwa domin gano mutanen da har yanzu ba a same su ba.
Sabon bayanin kwamishinan ’yan sandan ya nuna cewa jami’an tsaro sun ƙara takaita inda ake zargin sauran waɗanda aka sace suke, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
A wani mataki na ƙara ƙarfafa aikin, Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sandan da ke kula da ayyukan rundunar, DIG Shehu Nadada, zuwa Jihar Imo domin jagorantar aikin ceto da kuma tsara yadda za a gudanar da samamen.
Nadada ya isa jihar tare da kwamishinonin ’yan sanda biyu, inda ya duba yadda aka tura jami’an tsaro, dabarun gudanar da aikin da kuma kayan aikin da ake da su domin aikin ceto.
Rundunar ’yan sandan ta ce an ƙara tsaurara aikin bincike da ceto ta hanyar tura ƙarin rundunonin musamman da kayan aikin sintiri zuwa wuraren da aka gano, tare da amfani da bayanan sirri wajen bin sawun masu garkuwar da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

No comments