Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da buɗe shafinta na intanet domin ɗaukar mutanen da ke son yin aiki a matsayin ma’aikat...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da buɗe shafinta na intanet domin ɗaukar mutanen da ke son yin aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi yayin babban zaɓen 2027.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, inda ta ce an buɗe shafin INECPRES ga masu sha’awar neman aikin tun ƙarfe 8:00 na safe ranar 18 ga Satumbar 2026.
A cewar INEC, za a ci gaba da karɓar aikace-aikacen har zuwa tsakar dare na ranar Laraba, 18 ga Nuwambar 2026.
Hukumar ta ce shirin na INECPRES an buɗe shi ne domin mutanen da ke son yin aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi a lokacin babban zaɓen 2027 su samu damar neman aikin ta hanyar intanet.
Sanarwar ta ce: “Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta buɗe INECPRES ga masu neman aikin da ke son yin aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi yayin babban zaɓen 2027.”
Hukumar ta ƙara da cewa masu neman aikin za su iya yin rajistar ta shafinta na intanet, ko ta hanyar manhajar wayar hannu da kuma sigar shafin da ake amfani da kwamfuta wajen shiga.
A cewar hukumar, masu amfani da kwamfutar tafi-da-gidanka ko kwamfutar tebur za su iya shiga sigar yanar gizo ta INECPRES domin cike fom ɗin neman aikin.
Hukumar ta kuma ce masu amfani da wayoyin Android za su iya sauke manhajar INECPRES daga hanyoyin da ta tanada domin gudanar da aikace-aikacen.
INEC ta buƙaci duk masu sha’awar aikin da su yi amfani da hanyoyin da hukumar ta amince da su wajen cike takardun neman aikin, tare da tabbatar da cewa sun kammala aikace-aikacen kafin wa’adin rufewar shafin.
Buɗe wannan shafi na neman ma’aikatan wucin gadi na daga cikin matakan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ke ɗauka domin shirye-shiryen gudanar da babban zaɓen 2027.
.jpg)
No comments