Daga Zubairu Lawal, Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Asabar ya ƙaddamar da sabon titin Akwanga-Jos bypass mai tsawon ...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Asabar ya ƙaddamar da sabon titin Akwanga-Jos bypass mai tsawon kilomita 5.2 da aka kammala ginawa a ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da titin a Akwanga, Gwamna Sule ya bayyana aikin a matsayin muhimmin mataki da aka ɗauka domin rage cunkoson ababen hawa a garin Akwanga, tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a yankin.
Ya bayyana cewa sabon titin ya rage wa masu tafiya daga Keffi ko Gudi zuwa Jos tazarar da suke bi da fiye da kilomita biyar, tare da rage yawan haɗurran da ke faruwa akai-akai a cikin garin da kuma tsawaita rayuwar titunan cikin garin.
Gwamnan ya ce: “Wannan ya wuce titi kawai. Hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki. Tsawon shekaru, al’ummar Akwanga suna fama da cunkoson ababen hawa da haɗurra saboda duk motocin da ke zuwa Jos dole ne su ratsa tsakiyar garin.
“Yau, mun samar da wata hanya ta daban wadda za ta rage wa al’ummarmu wahala tare da buɗe sabbin wurare domin ci gaba.”
Ya bayyana cewa an gina titin ne bisa ƙa’idoji iri ɗaya da na babbar hanyar gwamnatin tarayya, domin ya iya ɗaukar manyan motocin dakon kaya.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin sanya fitilun hasken rana a titin domin tabbatar da tsaron masu amfani da hanyar a lokacin dare.
Gwamna Sule ya yabawa kamfanin da ya gudanar da aikin bisa kammala shi cikin lokacin da aka tsara kuma bisa ƙa’idojin da aka tanada.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta titunan cikin birane da na karkara a dukkan ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Haka kuma, Gwamna Sule ya ƙaddamar da tituna masu tsawon kilomita ɗaya kowanne a ƙananan hukumomin Akwanga, Nasarawa-Eggon da Wamba, waɗanda shugabannin ƙananan hukumomin suka gina.
Da suke jawabi daban-daban a ƙananan hukumominsu, shugabannin ƙananan hukumomin Akwanga, Nasarawa-Eggon da Wamba, Sadiyanu Isa-Andaha, Ilita Aliyu da Ezekiel Jaga, sun yabawa Gwamnan bisa bai wa ƙananan hukumomin jihar ’yancin gudanar da ayyukansu.
Sun ce: “Mun samu damar gudanar da waɗannan ayyuka da wasu da dama da aka kammala ko kuma ake ci gaba da gudanar da su ne saboda ’yancin da Gwamnan ya ba mu a ƙananan hukumomi.”
Shugabannin ƙananan hukumomin ukun sun yi alkawarin aiwatar da wasu ayyuka da za su shafi rayuwar al’umma kai tsaye a matakin ƙasa, domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatocin jiha da tarayya.
Shi ma kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na jihar, Yakuba Kwanta, ya ce sabon titin zai taimaka wajen samar da sabbin matsugunai da bunƙasa harkokin kasuwanci a gefen hanyar.
A nasa jawabin, Chun Mada, Samson Gamu-Yare, ya yabawa Gwamna Sule bisa wannan aiki, yana mai cewa sabon titin zai kawo ƙarshen wahalhalun da masu ababen hawa da mazauna Akwanga ke fuskanta a kullum.
Ya ce: “Garinmu ƙofa ce zuwa Arewa maso Gabas da Jihar Filato. Wannan titin zai ceci rayuka tare da kawo ci gaba kusa da al’ummarmu. Muna godiya.”
An gudanar da taron ƙaddamar da aikin ne tare da halartar Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Emmanuel Akabe; Sanata Danladi Halilu-Envulanza; sarakunan gargajiya; kwamishinoni; shugabannin jam’iyyar APC; da mazauna yankin.
No comments