Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsofaffin Abokan Siyasar El-Rufai Sun Koma APC, Sun Ce Shi Ne Ya Ci Amanar Su

Tsoffin abokan siyasa da magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun yi watsi da zargin cewa sun ci amanarsa, suna cewa a ...


Tsoffin abokan siyasa da magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun yi watsi da zargin cewa sun ci amanarsa, suna cewa a maimakon haka, shi ne ya yi watsi da fahimtar siyasar da ta haÉ—a su tun farko.

Matsayar Æ™ungiyar, wacce tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Mukhtar Isah Hazo, da wasu abokan siyasar suka sanya wa hannu, an raba wa ’yan jarida a Kaduna ranar Alhamis.

’Yan siyasar, Æ™arÆ™ashin Æ™ungiyar Kaduna De-Initiative, sun ce sun taÉ“a mara wa El-Rufai baya, yi masa kamfen tare da kare shi a siyasance, yayin da suke taimakawa wajen gina tsarin siyasa a faÉ—in jihar.

Sai dai sun ce dangantakar ta fara samun matsala ne sakamakon zargin ware wasu daga cikin abokan siyasar, saÉ“anin ra’ayi da kuma raguwar amincewar juna.

Ƙungiyar ta kuma sanar da komawarta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan wani yunÆ™urin sulhu da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jagoranta.

Ta ce matakin na komawa APC ya samo asali ne daga buƙatar su ɗauki alhakin makomar siyasarsu da ta magoya bayansu.

Daga cikin waÉ—anda suka sanya hannu ko suke da alaÆ™a da matsayar akwai tsohon Shugaban Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na Jihar Kaduna, kuma tsohon É—an Majalisar Dokokin jihar na Ungwan Sanusi sau huÉ—u, Nasiru Abdullahi Maikano.

Sauran sun haÉ—a da tsoffin kwamishinoni Ja’afaru Sani, Shehu Usman Makarfi da Abdu Kwari, da kuma tsohon Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da KuÉ—i, Bashir Saidu, wanda ya taÉ“a zama Babban Ma’aikacin Ofishin Gwamna (Chief of Staff) ga El-Rufai sau biyu.

Ƙungiyar ta Æ™aryata bayanin da ke cewa mambobinta ’yan siyasa ne da suka fusata kuma ke neman hanyar dawo da martabarsu a siyasa.

Ta ce, “Ba wasu ’yan siyasa ne kawai da suka fusata kuma ke neman hanyar samun matsayi a siyasa ba.

“Mambobinmu sun taÉ“a tsayawa takara, wasu sun ci zaÉ“e wasu kuma sun sha kaye. Sun tattara al’umma tare da gina alaÆ™ar siyasa a dukkan Æ™ananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba ita ce ta yi watsi da El-Rufai ba, sai dai tana ganin tsohon gwamnan ne ya yi watsi da fahimtar siyasar da ta ɗaure su tare.

“Ba mu yi watsi da El-Rufai ba; a maimakon haka, muna ganin El-Rufai ne ya yi watsi da fahimtar siyasar da ta haÉ—a mu,” in ji sanarwar.

Tsoffin abokan siyasar sun ce saÉ“anin da ya shiga tsakaninsu da El-Rufai ya fara bayyana sosai ne a wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan Kaduna, musamman bayan sake zaÉ“ensa a 2019.

Sun yi zargin cewa wasu daga cikin abokan siyasar tsohon gwamnan sun fara jin an mayar da su gefe wajen yanke muhimman shawarwarin gwamnati.

Haka kuma, sun zargi wasu daga cikin ’yan gidan El-Rufai da fara samun Æ™arin tasiri a harkokin gudanar da gwamnati.

“Ba mu taÉ“a Æ™orafin cewa El-Rufai ya dogara da ’yan gidansa ko wasu amintattun mutanensa ba. Abin da ya dame mu shi ne yadda tasirin muradun iyali ya fara Æ™aruwa, yayin da tsarin siyasar da ya tallafa wa gwamnatin ya fara yin rauni,” in ji su.

A cewar ƙungiyar, dangantakar ta riga ta tsananta sosai zuwa shekarar 2023, sannan ta ƙara lalacewa bayan El-Rufai ya bar kujerar gwamna.

Ta ce batun siyasar zaÉ“en gwamnan Kaduna na 2027 a Æ™arÆ™ashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) shi ne ya kawo Æ™arshen alaÆ™ar siyasar da ke tsakaninsu.

Ƙungiyar ta ce tsohon Kwamishina Ja’afaru Sani shi ne É—an siyasar da É“angaren nasu ya fi son ya gaje su a takarar gwamna, kuma shi ne wanda aka tsara za a gina tsarin siyasar su a kansa domin zaÉ“en 2027.

“Ja’afaru Sani shi ne mutumin da ake sa ran tsarin siyasarmu zai tattaru a kansa domin takarar gwamna a 2027,” in ji sanarwar.

Sai dai ƙungiyar ta yi zargin cewa El-Rufai ya zaɓi mara wa tsohon abokin hamayyarsa a siyasa, Isa Ashiru, baya a zaɓen fidda gwani na ADC.

“Maimakon ya goyi bayan tsarin siyasar da muka gina, El-Rufai ya zaÉ“i mara wa Isa Ashiru baya, wanda a baya ya kasance abokin hamayyarsa na siyasa,” in ji Æ™ungiyar.

Daga baya Ashiru ya lashe zaÉ“en fidda gwani na ADC da Æ™uri’u 86,113, yayin da Ja’afaru Sani ya samu Æ™uri’u 29,580.

Sai dai Sani ya Æ™i amincewa da sakamakon, yana zargin an samu kura-kurai da rashin bin Æ™a’ida a lokacin zaÉ“en.

Tsoffin abokan siyasar El-Rufai sun kuma yi zargin cewa goyon bayan da ya bai wa Ashiru yana da alaƙa da yunƙurin ci gaba da riƙe tasirinsa a siyasa idan har ADC ta kafa gwamnati a Kaduna.

Sun kuma yi wani zargi cewa an yi wata fahimta ta siyasa da za a naɗa wasu daga cikin matan El-Rufai guda biyu mukamai a gwamnati idan ADC ta lashe zaɓen.

Sai dai Æ™ungiyar ta amince cewa ba a tabbatar da wannan zargi a gaban wata kotu ba, kuma babu wata yarjejeniya a rubuce da aka gabatar wa jama’a da za ta tabbatar da shi.

A nasu ra’ayin, tsoffin abokan siyasar sun ce bai kamata a É—auki biyayya ga É—an siyasa a matsayin wani bashi na dindindin da dole sai an biya shi ba.

Sun ce El-Rufai yana da ’yancin yin zaÉ“in siyasar da ya ga dama, kamar yadda su ma suke da ’yancin yin nasu zaÉ“in.

“Ba za a É—auki biyayyar siyasa a matsayin wani bashi na dindindin ba. El-Rufai yana da ’yancin yin zaÉ“in siyasarsa, mu ma muna da ’yancin yin namu,” in ji su.

Haka kuma, sun yi watsi da ra’ayin cewa El-Rufai shi kaÉ—ai ne ya gina tsarin siyasar da ya kai shi ga samun nasarar zaÉ“e a Kaduna.

“Ba El-Rufai ne ya Æ™irÆ™iri siyasar Kaduna daga farko ba. Akwai ’yan siyasa, masu shirya harkokin siyasa a matakin Æ™asa, tsoffin zaÉ“aɓɓun jami’ai da kuma tsare-tsaren siyasa da aka riga aka kafa tun kafin El-Rufai ya zama babban jigo a siyasar jihar,” in ji Æ™ungiyar.

Ta kawo Bashir Saidu a matsayin É—aya daga cikin mutanen da suka taka rawa wajen gina wannan tsarin siyasa tun kafin fitowar El-Rufai a matsayin babban É—an siyasar Kaduna.

Daga baya Saidu ya zama kwamishina a gwamnatin El-Rufai sannan ya riÆ™e matsayin Babban Ma’aikacin Ofishin Gwamna sau biyu.

Ƙungiyar ta ce sabon sauyin matsayinta na siyasa ya samo asali ne daga buƙatar sake tsara makomarta tare da mutanen da suke goyon bayanta, musamman bayan abubuwan da suka faru a shekarun baya.
 

No comments