Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa ta ƙaddamar yana kawo sauyi a fannoni daban-daban ma...
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da aka fara jerin bukukuwa da ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa domin bikin cikar Jihar Zamfara shekaru 30 da kafuwa.
An gudanar da bikin ne tare da ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa, inda suka samu halartar tsohon Shugaban Mulkin Soja na farko na Jihar Zamfara, Kanar Jibril Bala Yakubu (mai ritaya), da tsoffin gwamnonin jihar, Ahmed Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi, da sauran manyan baki.
Da yake jawabi a bikin fareti na Ranar ’Yancin Kai ta Ƙasa da kuma bikin cikar Zamfara shekaru 30 a filin Trade Fair Complex da ke Gusau, Gwamna Lawal ya ce jihar ta rabu da zaman ƙuncin baya, inda yanzu ta shiga wani sabon yanayi na aiwatar da ayyuka a aikace, gaskiya da rikon amana, da kuma samun ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce, “A yau muna tare da sauran ’yan Nijeriya wajen bikin Ranar ’Yancin Kai, sannan muna cika shekaru 30 da kafuwar Jihar Zamfara a ranar 1 ga Oktoba, 1996.
“Mun gode wa Allah bisa rahamarsa, jinƙansa da kariyar da ya yi mana, waɗanda suka jagorance mu a lokutan ƙalubale da nasarori, tare da haɗa mu wuri guda a ƙarƙashin makoma ɗaya.
“Yayin da muke kallon jaruman jami’an tsaronmu, hukumomin tsaro na farar hula, ɗalibai da matasanmu masu ƙwazo suna gudanar da fareti cikin haɗin kai a wannan fili, hakan ya tunatar da mu irin juriyar da ke cikin ruhin ɗan Nijeriya, musamman kuma ƙarfin hali da ɗabi’un mutanenmu.
“Ya kamata mu yi tunani sosai kan manyan sadaukarwar da iyayenmu da suka kafa wannan ƙasa suka yi. Sun yi gwagwarmaya ba tare da gajiyawa ba wajen karya kangin mulkin mallaka tare da samar da ƙasa mai ’yanci da cikakken iko kan kanta.
“Muna bin su bashin godiya na har abada saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen kare haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da cikakken ikon Nijeriya kan ƙasarta.
“Yayin da muke kallon shekaru goma masu zuwa, dole ne mu fahimci cewa ’yancin kai na gaskiya yana buƙatar ɗaukar nauyi tare.
“Gwamnati ita kaɗai ba za ta iya yin komai ba. Ina kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini, ma’aikatan gwamnati, ’yan kasuwa da matasanmu masu juriya da su haɗa kai.
“Dole ne mu ajiye bambance-bambancen ƙabila, siyasa da mazhaba a gefe, mu kare zaman lafiyar da kakanninmu suka yi gwagwarmaya domin samunsa.”
A ranar Juma’a kuma, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kashi na uku na aikin gyara da zamanantar da Sakatariyar J.B. Yakubu da ke Gusau.
An ce aikin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake gina cibiyoyin gwamnati tare da samar da ma’aikatan gwamnati na zamani, masu inganci, amfani da fasahar zamani wajen gudanar da aiki, kuma masu mayar da hankali kan samar da sakamako.
Sakatariyar J.B. Yakubu na ɗauke da wasu muhimman Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs), waɗanda ke da alhakin gudanar da ayyuka kusan a dukkan fannoni na mulki da samar da hidimomin jama’a.
Gwamna Lawal ya ce zamanantar da sakatariyar zai ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, ƙarfafa sadarwa da haɗin kan cibiyoyin gwamnati, tare da taimakawa wajen aiwatar da manufofin gwamnati cikin sauri da inganci.
Ya ce, “Bikin na yau yana da muhimmanci, musamman ganin mun tarbi Mai Girma Kanar Jibril Bala Yakubu (mai ritaya), Shugaban Mulkin Soja na farko na Jihar Zamfara, wanda aka sanya wa wannan sakatariya sunansa.
“Yayin da Zamfara ke bikin cikar shekaru 30 da kafuwarta, ya dace shugaba daga cikin waɗanda suka kafa tushen jihar ya kasance a nan domin ganin wannan gagarumar nasara.”
Da yake jawabi tun da farko, tsohon Shugaban Mulkin Soja na farko na Jihar Zamfara, Kanar Jibril Bala Yakubu (mai ritaya), ya yaba wa Gwamna Lawal kan manyan ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar, musamman a fannonin gine-gine, ilimi da kiwon lafiya.
A ranar Juma’a ɗin nan kuma, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, CFR, mni, ya ƙaddamar da sabon masallacin Juma’a na Yardole da aka sake ginawa tare da gyara shi, da kuma katafaren rukunin shagunan kasuwanci da aka haɗa da masallacin.
An sanya wa masallacin sunan Malam Sambo Dan Ashafa, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma abokin babban Mujaddadi kuma jagoran Jihadin Sakkwato na farko, Sheikh Usmanu bn Fodiyo.
Bayan gudanar da ibada, masallacin zai kuma kasance cibiyar koyar da ilimin Musulunci da gudanar da bincike, domin ƙara bunƙasa ilimi da nazari a fannin addini.
SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
Oktoba 2, 2026








No comments