A yau ne za a fara jigilar jirgin saman kasuwanci na farko tsakanin Abuja da Gusau yayin da Zamfara ke bikin cika shekaru 30 da kafuwarta. J...
A yau ne za a fara jigilar jirgin saman kasuwanci na farko tsakanin Abuja da Gusau yayin da Zamfara ke bikin cika shekaru 30 da kafuwarta.
Jirgin farko na kasuwanci zai tashi ne daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Kamfanin jiragen sama na XeJET ne zai gudanar da wannan jirgin, wanda zai kasance na farko na kasuwanci da zai isa Zamfara cikin shekaru 30 da kafuwar jihar.
Bayan fara zirga-zirgar, kamfanin zai riÆ™a gudanar da tashin jirage biyu a kowane mako daga Abuja zuwa Gusau, wato ranar Litinin da Juma’a.
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya gina filin jirgin ne da nufin sauÆ™aÆ™a zirga-zirga zuwa jihar tare da buÉ—e Æ™arin damarmaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da sauran baÆ™i.
A wani mataki na ƙara sauƙaƙa wa fasinjoji amfani da filin jirgin, gwamnatin jihar ta samar da intanet kyauta, wato Free WiFi a muhimman sassan filin jirgin, ciki har da wuraren tashi da saukar jiragen cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ɗakunan tarbar manyan baƙi, wato VIP, hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama, tashar kashe gobara da sauran wuraren gudanar da ayyuka.
Gwamna Lawal ya kuma amince da samar da motocin haya kyauta ga dukkan fasinjojin da za su yi amfani da filin jirgin.
A cewar jadawalin shirye-shiryen bikin cika shekaru 30 da kafuwar jihar, bayan saukar jirgin farko na kasuwanci, za a gudanar da gagarumin fareti a filin Trade Fair Complex da ke Gusau.
Daga nan za a gudanar da liyafar cin abinci ta musamman da yamma a Nadabo Hall, J.B. Yakubu Secretariat da ke Gusau.
A rana ta biyu ta bikin, za a ƙaddamar da Sashen Uku na Sakatariyar J.B. Yakubu da aka gyara tare da samar mata da kayan aiki.
Bayan haka kuma, za a Æ™addamar da Masallacin Juma’a na Sambo Dan Ashafa da ke Gusau.
A wani taron manema labarai da ya gudanar jiya a Gusau, Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Abubakar Nakwada, ya ce bikin cika shekaru 30 zai ba jihar damar waiwayar tafiyar da ta yi cikin shekaru uku da suka gabata, girmama waÉ—anda suka bayar da gudunmawa wajen ci gabanta da kuma tsara sabuwar alkiblar ci gaba mai É—orewa.
Nakwada ya ce tarihin Zamfara na shekaru 30 mallakin dukkan gwamnatocin da suka jagoranci jihar ne, sarakunan gargajiya, hukumomi, ma’aikatan gwamnati da sauran ’yan Æ™asa da suka taka rawa wajen ci gaban jihar tun bayan kafuwarta a shekarar 1996.
Ya ce sauye-sauyen da aka samu cikin sauri a Zamfara a cikin shekaru uku da suka gabata ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal sun yi matuƙar yawa.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, gwamnatin Lawal ta aiwatar da matakai a fannonin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, noma, ababen more rayuwa, bunÆ™asa Æ™warewar jama’a, gyaran hukumomi da bunÆ™asa tattalin arziki.
A cewarsa, manufar gwamnatin ba wai kawai gina ayyuka ba ce, illa magance matsalolin ci gaba da suka daɗe suna addabar jihar, ƙarfafa hukumomin gwamnati da kuma kafa tsarin da zai tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Nakwada ya ce Zamfara ta shafe shekaru tana fama da hare-haren ’yan bindiga, sace-sacen mutane da kuma lalacewar sana’o’in karkara, lamarin da ya sa dawo da tsaro ya zama muhimmin mataki wajen sake gina al’ummomi.
Ya ce inganta tsaro zai taimaka wajen mayar da manoma gonakinsu, farfaÉ—o da harkokin tattalin arziki da kuma dawo da amincewar jama’a.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce gwamnati na ci gaba da ba Rundunar Sojin Najeriya, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Ƙasa (DSS), Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar gagarumar gudunmawa.
Ya ce tallafin ya haɗa da motocin aiki, motocin sulke, jirage marasa matuƙa na sa ido, babura na musamman da sauran kayan aiki da ake buƙata domin inganta zirga-zirga, sa ido, tattara bayanan sirri da kuma gaggauta kai ɗauki yayin da ake fuskantar barazana.
Dangane da adana tarihin jihar kuwa, Nakwada ya ce za a gabatar da wani cikakken kundin tarihin Jihar Zamfara a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen bikin cika shekaru 30.
Ya ce kundin zai Æ™unshi tarihin jihar, shugabanninta, hukumominta, al’ummarta, yadda ta samu ci gaba da kuma manyan abubuwan da suka faru tun kafuwarta a shekarar 1996 zuwa 2026.

No comments