Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Manoma Da Masu Samar Da Hatsi Ta Naɗa Ibrahim Masari A Matsayin Uban Ƙungiya

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Wasu Batutuwa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya karɓi shugabanni da mambobin Ƙungiyar...

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Wasu Batutuwa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya karɓi shugabanni da mambobin Ƙungiyar Manoma da Masu Samar da Hatsi ta Amana Farmers and Grains Suppliers Association of Nigeria a ofishinsa da ke Abuja, inda ƙungiyar ta naɗa shi a matsayin Uba gare ta.

A cikin wata sanarwa da Ishaq Samaila daga Ofishin Yaɗa Labarai na Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa da Wasu Batutuwa ya sanya wa hannu, an bayyana cewa taron na daga cikin shawarwari da ake ci gaba da yi da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen 2027.

Sanarwar ta ce a yayin taron, ƙungiyar ta bayyana aniyarta ta tattara mambobinta da sauran hanyoyin sadarwarta domin marawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya.

A yayin ganawar, ƙungiyar ta kuma naɗa Alhaji Ibrahim Kabir Masari a matsayin Babban Uban Ƙungiyar, a matsayin girmamawa ga irin jagorancin da yake nunawa da kuma hulɗarsa da masu ruwa da tsaki a matakin ƙasa da ƙasa, musamman al’ummomin tushen siyasa.

Tawagar ƙungiyar ta samu jagorancin Shugabanta na Ƙasa, Alhaji Haruna Ahmed Pambeguwa.

Taron ya samu halartar Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Dakta Muttaka Rabe Darma; Mai Gudanar da Shirin Sabuwar Haɗin Kan Afirka (NEPAD), Jabiru Abdullahi Tsauri; Babban Ma’aikacin Ofishin Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Farfesa Mohammad Kabir Isa; da Mai Bai wa Alhaji Ibrahim Kabir Masari Shawara na Musamman, Honourable Yahaya Bello, tare da sauran mambobin ƙungiyar da masu ruwa da tsaki.

Da yake magana a madadin ƙungiyar, Alhaji Haruna Ahmed Pambeguwa ya gode wa Alhaji Ibrahim Kabir Masari bisa karɓar tawagar da kuma ba su damar tattaunawa kai tsaye da shi.

A nasa martanin, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya gode wa ƙungiyar bisa karramawar da ta yi masa, tare da maraba da shugabanninta da mambobinta.

Masari ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ƙara kusantar jama’a da ci gaba da yin shawarwari da masu ruwa da tsaki yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
 

No comments