Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙaruwar Ajiyar Kuɗaɗen Waje Na Da Nasaba Da Tulin Kuɗaɗen Da ‘yan Nijeriya Ke Turawo Gida Daga Waje Da Ƙarin Shigowar Masu Zuba Jari -CBN

  • Ya sake jaddada aniyar tabbatar da daidaiton farashi Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya danganta ƙaruwar da ajiyar ku...


• Ya sake jaddada aniyar tabbatar da daidaiton farashi

Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya danganta ƙaruwar da ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar nan ya yi cewa hakan na da nasaba da ƙarin shigowar kuɗaɗen waje cikin ƙasa daga 'yan Nijeriya mazauna ƙasashe daban-daban, sai kuma ƙarin kuɗaɗen waje da ke shigowa daga masu sha'awar zuba jari a cikin ƙasar nan.

Daraktar Sashen Hulɗa da Masu Ruwa da Tsaki da Hulɗa da Hukumomi na CBN, Hajiya Hakama Sidi-Ali ce ta bayyana hakan, ta kuma jaddada yadda ajiyar kuɗaɗen waje ke ƙaruwa, inda ta kai dala biliyan 55.25 a ranar 18 ga Satumba, 2026, matakin da ya kasance mafi girma cikin shekaru 18.

Hajiya Hakama ta yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, yayin bikin “Ranar Musamman ta CBN” a bikin bajekolin kasuwanci na ƙasa da ƙasa na Abuja karo na 21 da yanzu haka ake gudanarwa.

Daraktar ta CBN ta danganta ƙarfafa matsayin ajiyar kuɗaɗen waje da matakan da aka ɗauka domin inganta shigowar kuɗaɗen waje da kuma mayar da ƙarin hada-hadar kuɗi zuwa hanyoyin hukuma.

Ta ce wannan ci gaba ya nuna tasirin sauye-sauyen da aka aiwatar domin ƙarfafa kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya ke turowa gida, jawo masu zuba jari daga wa waje, da kuma faɗaɗa shigar mutane cikin tsarin hada-hadar kuɗi na hukuma.

A cikin ‘yan watannin nan, CBN ya sha bayyana farfaɗowar kuɗaɗen da ake turawa ta hanyoyin hukuma a matsayin muhimmin ɓangare na sake gina ajiyar kuɗaɗen waje.

Ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen waje ta kuma zo ne a daidai lokacin da matsin-lamba kan kasuwar canjin kuɗaɗen waje ke raguwa, tare da ƙarfafa muhimman ginshiƙan tattalin arzikin waje.

Hakama ta ce haɗa kasuwannin canjin kuɗaɗen waje wuri guda ya taimaka wajen ƙarfafa daidaito, inganta amincewar masu zuba jari da kuma rage karkatar da tsarin. Ta ce hakan ya zo ne tare da wasu sauye-sauye, ciki har da sake fasalin jarin bankuna da kuma 'Payments System Vision 2028', wanda aka tsara domin zurfafa tsarin biyan kuɗi na zamani da na tsakanin ƙasashe.

Ta bayyana cewa ƙarfafa matsayin tattalin arzikin waje na ƙasar nan na daga cikin ginshiƙan da za su taimaka wajen gina tattalin arziki mai jure wa ƙalubale.

A cewar ta, “Ciniki mai jure wa ƙalubale yana bunƙasa ne a cikin yanayin da tattalin arzikin ƙasa yake da daidaito.”

Daga nan ta jaddada cewa ‘yan kasuwa sun fi samun ƙarfin gwiwar tsara harkokin su da zuba jari a lokacin da hauhawar farashi ke raguwa, farashin canjin kuɗi yana da ɗan daidaito, sannan tsarin hada-hadar kuɗi yana da ƙarfi.

Daraktar ta CBN ta ce manufar ba wai kawai tara ajiyar kuɗaɗen waje ba ce, illa ƙirƙirar yanayin tattalin arziki da zai bai wa ‘yan kasuwa damar faɗaɗa samar da kayayyaki, jawo jarin waje da kuma yin gogayya a kasuwa.

CBN dai ya rage Adadin Ribar Manufofin Kuɗi (MPR) daga kashi 26.5 zuwa kashi 23. Wannan mataki ne Hakama ta ce an ɗauki matakin ne domin tallafa wa harkokin samar da kayayyaki da ayyukan tattalin arziki, yayin da aka ci gaba da mayar da hankali wajen rage hauhawar farashi, wanda a halin yanzu yake kashi 15.39, zuwa matakin ƙasa da kashi 10.

Daraktar ta CBN ta sake tabbatar da aniyar bankin  wajen inganta tsarin hada-hadar kuɗi baki ɗaya. Ta kuma buƙaci ‘yan kasuwa su ƙirƙiro sabbin dabaru, su inganta shugabanci da gudanarwa, tare da neman sabbin kasuwanni.

Kyakkyawan Hasashen Bankin Duniya Kan Tattalin Arzikin Nijeriya:

Sabon hasashen da Bankin Duniya ya yi ya zo ne bayan da Nijeriya ta samu kyakkyawan sakamako a fannin bunƙasar Babban Tattalin Arzikin Ƙasa (GDP), wato Ƙarfin Tattalin Arzikin Cikin Gida.

Bisa bayanan Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS), GDP na Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.43 bisa ɗari a zahiri daga shekara zuwa shekara a rubu’i na biyu na 2026, wato a watannin Afrilu, Mayu da Yuni,
idan aka kwatanta da kashi 4.23 a makamancin rubu’in na shekarar 2025.

Ƙaruwar kashi 4.43 ta nuna ci gaba idan aka kwatanta da kashi 4.23 da aka samu a rubu’i na biyu na 2025.

Wannan sabon sakamako ya samar da wani sabon ma’auni na cikin gida da ke nuna faɗaɗar tattalin arziki da sabon hasashen Bankin Duniya ya bayyana.

Gabaɗaya, bankin ya nuna cewa bunƙasar tattalin arzikin yankin na samun tallafi daga ƙarin juriyar tattalin arziki, ƙarfafa buƙatun cikin gida da kuma ƙarin zuba jari a fasahohin zamani, baya ga sauyin makamashi da ke faruwa a duniya.
 

No comments