Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gobara Ta Laƙume Rayuka 65, Tare Da Asarar Dukiya Ta Sama Da Naira Biliyan 13

Aƙalla mutane 65 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobara da wasu iftila’i a Jihar Legas tsakanin watan Janairu da Satumba na shekarar 2026, ...


Aƙalla mutane 65 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobara da wasu iftila’i a Jihar Legas tsakanin watan Janairu da Satumba na shekarar 2026, yayin da dukiyoyin da suka lalace suka kai Naira biliyan 13.24.

Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas ce ta bayyana hakan a rahotonta na ayyukan zango na uku na shekarar 2026, inda ta ce ta tunkari aukuwar iftila’i daban-daban guda 1,324 cikin watanni tara.

Rahoton ya nuna cewa daga cikin waɗannan lamuran, gobara ce ta fi yawa, inda aka samu aukuwar gobara guda 1,135. Haka kuma, jami’an hukumar sun yi nasarar ceto mutane 210 da rai, yayin da aka gano gawarwakin mutane 65 da ake zargin sun mutu a yayin ayyukan ceto.

A cewar rahoton da babbar jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Fadairo Maria, ta fitar, lamuran sun haɗa da kiran neman agajin gobara guda 1,135, ayyukan ceto mutane guda 79, ayyukan kuɓutar da dukiyoyi guda 100, aukuwar rushewar gine-gine guda tara da fashewar iskar gas guda ɗaya.

Binciken alkaluman kowane wata ya nuna cewa watan Janairu ne ya fi yawan aukuwar iftila’i, inda aka samu lamura guda 203, sai watan Maris da guda 201. A watan Satumba ne aka samu mafi ƙarancin lamura, inda adadin ya tsaya kan 94.

Haka kuma, watan Maris ne ya fi yawan kiran neman agajin gobara, inda aka samu guda 176, sai Janairu da guda 173. Satumba ya kasance watan da aka fi samun ƙarancin kiran gobara, inda aka samu guda 80 kacal.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an samu kiran neman agajin gaggawa na ƙarya guda 341 a cikin lokacin da ake nazari. Ta yi gargaɗin cewa irin waɗannan kiraye-kirayen na iya jinkirta isar jami’an kashe gobara zuwa wuraren da aka samu ainihin haɗari, lamarin da ka iya jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.

Babbar shugabar hukumar, Margaret Adeseye, ta ce waɗannan alkaluma sun nuna muhimmancin ci gaba da wayar da kan jama’a game da matakan kariya daga gobara, sanar da hukumomi da wuri idan wani haɗari ya faru, da kuma bin ƙa’idojin tsaro yadda ya kamata.

Adeseye ta shawarci mazauna jihar da su guji kunna wuta ba bisa ƙa’ida ba, su riƙa adana kayayyakin da ke saurin kamawa da wuta yadda ya dace, tare da kashe na’urorin lantarki da cire su daga wutar lantarki idan ba a amfani da su.

Ta kuma gargaɗi jama’a kan haɗa na’urorin lantarki da yawa a soket guda fiye da ƙimarsu, saboda hakan na iya haddasa gobara.

Bugu da ƙari, ta bukaci gidaje, kamfanoni da cibiyoyi da su tabbatar da cewa na’urorin kashe gobara suna aiki yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa hanyoyin fita yayin aukuwar haɗari da wuraren da jami’an agaji ke bi ba su toshe ba.

Dangane da asarar tattalin arziki, hukumar ta bayyana cewa dukiyoyin da aka yi nasarar kuɓutarwa daga lalacewa sun kai kimanin naira biliyan 79.44, yayin da asarar da aka yi ta kai naira biliyan 13.24.

Hukumar ta kiyasta cewa jimillar kuɗin dukiyoyin da lamarin ya shafa ya kai naira biliyan 92.68.

Adeseye ta sake jaddada cewa kiran neman agajin gaggawa na ƙarya na iya haifar da mummunan sakamako, musamman idan ya jinkirta kai ɗauki ga mutanen da ke cikin haɗari na gaske.

Ta ce irin waɗannan kiraye-kirayen na iya hana jami’an kashe gobara isa wuraren da ake buƙatar agajinsu cikin gaggawa, tare da jefa rayuka, dukiyoyi da muhalli cikin haɗari.

Saboda haka, ta buƙaci mazauna jihar da su riƙa sanar da hukumomi da zarar gobara ta tashi, tare da ba jami’an agajin gaggawa haɗin kai idan sun isa wurin da abin ya faru.

Babbar shugabar ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta hanyar gaggauta kai ɗauki, hana aukuwar gobara, wayar da kan al’umma, tabbatar da bin ƙa’idojin kariya daga gobara da kuma ƙarfafa hulɗa da al’ummomi.

Ta jaddada cewa rigakafi da ɗaukar matakan kariya tun da wuri su ne hanyoyin da suka fi tasiri wajen rage mummunan illar gobara.

No comments