Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kama jami’anta biyu da ke kmbakin aiki da wani tsohon jami'i da aka sallama daga aiki, bisa zargin karɓ...
Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kama jami’anta biyu da ke kmbakin aiki da wani tsohon jami'i da aka sallama daga aiki, bisa zargin karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba daga masu ababen hawa a kusa da mahaɗar Transcorp da ke Maitama, Abuja.
An kama waɗanda ake zargin ne a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, bayan rundunar ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 2:50 na rana, inda aka kai ƙorafin cewa wasu jami’an ’yan sanda da ke aiki a yankin na karɓar kuɗi daga masu ababen hawa ba bisa ƙa’ida ba.
Bayan samun ƙorafin, jami’an ’yan sanda daga ofishin Maitama sun garzaya wurin, inda aka tura tawagar bincike ƙarƙashin jagorancin Jami’in Binciken Laifuka na sashe, mai muƙamin DCO 4, domin gudanar da bincike kan zargin.
Daga bisani, an kama mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin.
An bayyana sunayensu a matsayin ASP Michael Godwin, mai lambar aiki AP No. 188981, wanda ke aiki a sashen sufuri na rundunar da ke hedikwatar ’yan sanda a Abuja; Sufeto Demeka’a Yarkwan, mai lambar aiki AP No. 346638, wanda ke aiki a ofishin ’yan sanda na Wuse; da Sajan William Udokang, tsohon jami’in rundunar da aka sallama daga aikin ’yan sanda.
Binciken ya ɗauki sabon salo ne bayan jami’an ’yan sanda sun gano lasisin tuƙi guda 15 a hannun waɗanda ake zargin.
Binciken farko ya nuna cewa lasisin na mutane daban-daban ne, kuma babu ɗaya daga cikinsu da aka yi wa rajista da sunan wani daga cikin mutanen uku da aka kama.
Samun waɗannan lasisi ya sa masu bincike fara ƙoƙarin gano yadda takardun suka shiga hannun waɗanda ake zargin, da kuma yanayin da aka karɓe su daga masu ababen hawa.
Rahotanni sun nuna cewa masu binciken sun tuntubi wasu daga cikin masu lasisin da kuma danginsu na kusa, a wani mataki na gano yadda takardun suka shiga hannun jami’an.
Bayanan farko da aka tattara yayin binciken sun nuna cewa ana zargin wasu daga cikin masu ababen hawan an karɓe lasisin tuƙinsu, sannan aka nemi su biya kuɗi kafin a mayar musu da takardun.
Rahotanni sun ce kuɗin da ake zargin an karɓa sun kasance tsakanin Naira 50,000 da Naira 183,000, gwargwadon yanayin kowanne lamari.
Sai dai binciken ’yan sanda bai kammala ba, kuma hukumomin na ƙoƙarin gano tare da tuntubar dukkan masu lasisin tuƙi 15 da aka samu.
Ana kuma sa ran masu binciken za su sake karɓar bayanai daga bakin masu ababen hawan da abin ya shafa, domin fayyace yadda kowane lamari ya faru da kuma tantance sahihancin zarge-zargen.
Lamarin ya sake jawo hankalin jama’a kan zarge-zargen karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da sauran munanan halaye da ake dangantawa da wasu jami’an tsaro.
Kasancewar biyu daga cikin waɗanda ake zargin jami’an ’yan sanda ne da ke kan aiki, yayin da na ukun tsohon jami’i ne da aka sallama, ya ƙara jawo hankalin jama’a kan yadda binciken zai gudana.
Rahotanni sun ce ofishin ’yan sanda na Maitama ya riga ya aika da rahoton abin da ya faru ga manyan jami’an rundunar domin samun ƙarin umarni da ɗaukar matakan da suka dace.
Ya zuwa yanzu, rundunar ’yan sandan ba ta bayyana sakamakon ƙarshe na binciken ba.
A halin yanzu, zarge-zargen da ake yi wa mutanen ukun ba su tabbata a gaban doka ba. Ana ɗaukar su a matsayin marasa laifi har sai kotun da ta dace ta same su da laifi.

No comments