Daga Zubairu Lawal, Lafia Kwamitin Zartarwa da Majalisar Ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Nasarawa, sun dakatar d...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Kwamitin Zartarwa da Majalisar Ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Nasarawa, sun dakatar da shugabar ƙungiyar, Comrade Mercy Tanze Zabadi, bisa zargin rashin gaskiya wajen gudanar da harkokin kuɗi da kuma yin amfani da ofishinta ba bisa ƙa’ida ba.
Sanarwar dakatarwar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ƙungiyar, Comrade Esther Anna, ta sanya wa hannu, wadda aka miƙa wa jaridar manema Labarai a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.
Sanarwar ta bayyana cewa an cimma matsayar dakatar da Comrade Mercy Tanze Zabadi ne a wani taron majalisar ƙungiyar da aka gudanar a Lafia, bayan tattaunawa mai zurfi kan ayyukan shugabar, waɗanda ake zargin sun saɓa wa kundin tsarin mulkin NAWOJ da kuma ƙa’idar shugabanci na bai ɗaya.
“Bisa la’akari da abubuwan da aka bayyana a sama, majalisar ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da Comrade Mercy Tanze Zabadi daga muƙamin shugabar ƙungiyar.
Haka kuma, ta miƙa ƙorafi ga sakatariyar ƙasa ta NAWOJ domin kafa kwamitin binciken gaskiya don gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi mata.”
Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma kyakkyawan shugabanci a ƙungiyar.
Comrade Mercy Tanze Zabadi, wadda take cikin sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ’yan jarida, an zaɓe ta a matsayin shugabar NAWOJ ta Jihar Nasarawa a watan Satumban shekarar da ta gabata.
mataimakiyar shugabar ƙungiyar, Comrade Amina Mohammed, ta karɓi ragamar shugabancin NAWOJ a Jihar Nasarawa, har sai an kammala bincike kan zarge-zargen da ake yi wa shugabar da aka dakatar.

No comments