Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Aka Kashe Wani Ɗan Achaba A Kaduna, Aka Gudu Da Babur Ɗin

Wani mai tuƙin babur ya rasa ransa bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun caka masa wuƙa a yankin Barnawa da ke Jihar Kaduna, tare da yin ...




Wani mai tuƙin babur ya rasa ransa bayan wasu da ba a san ko su waye ba sun caka masa wuƙa a yankin Barnawa da ke Jihar Kaduna, tare da yin awon gaba da babur ɗinsa.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2026, a kan titin Gongola, kusa da cibiyar taruka ta ProView Event Center.

Bayanan da ake da su sun nuna cewa maharin ko maharan sun ƙwashe babur ɗin mamacin bayan sun kai masa harin, yayin da suka bar wayarsa ta hannu a wurin.

Rahotanni sun kuma ce jami’an Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da ke aiki a ofishin Barnawa sun tuntubi iyalan mamacin bayan faruwar lamarin. An ce babban yayansa da limamin cocinsa sun isa wurin bayan an sanar da su abin da ya faru.

Sai dai har yanzu ba a fayyace cikakken bayani kan kisan ba, ciki har da sunan mamacin, dalilin kai masa harin da kuma ko an kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

No comments