Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Farashin Fetur A Gidajen NNPCL Na Wata Guda

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin sayar da man fetur a farashi mai rangwame a gidajen man NNPCL na tsawon kwanaki 30, a wani mataki na ra...

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin sayar da man fetur a farashi mai rangwame a gidajen man NNPCL na tsawon kwanaki 30, a wani mataki na rage wa ’yan Najeriya da ’yan kasuwa radadin hauhawar farashin makamashi da sufuri. Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da sabbin matakan gwamnati na rage tsadar rayuwa. 

A cewar Oyedele, za a fara amfani da rangwamen ne a gidajen sayar da man NNPCL, inda aka tsara bai wa masu motocin haya da safarar jama’a fifiko, domin rage musu kuÉ—in da suke kashewa wajen sayen fetur. Ya ce manufar matakin shi ne samar da sauÆ™i cikin gaggawa ga masu sufuri da fasinjoji da ke fuskantar Æ™arin kuÉ—in sufuri sakamakon tsadar man fetur. 

Ministan ya kuma bayyana cewa wannan mataki ba komawar tallafin fetur ba ne, yana mai cewa gwamnati tana son samar da rangwame na wucin gadi tare da É—aukar wasu matakai na rage sauyin farashin makamashi. Daga cikin sauran shirin akwai tattaunawar kafa iyakar farashin saukar da fetur zuwa N1,350 kan lita, wadda za a riÆ™a duba ta duk wata bisa yanayin kasuwa. 

Gwamnatin ta ce tana kuma Æ™ara mayar da hankali kan CNG da sauran hanyoyin makamashi masu rahusa, domin rage dogaro da fetur da kuma sauÆ™aÆ™a kuÉ—in sufuri. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayyana cewa ana son faÉ—aÉ—a amfani da CNG domin rage kuÉ—in sufuri, tare da tabbatar da cewa amfanin makamashi mai rahusa ya isa ga ’yan Najeriya ta hanyar rage kuÉ—in hawa.
 

No comments