Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Idris Ya Yaba Wa Bago Kan Ayyukan Raya Neja, Ya Jinjina Wa Aikin Hanyar Tarayya Na ₦1.5tn

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, kan zuba jari a harkokin n...

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, kan zuba jari a harkokin noma da gine-ginen ababen more rayuwa, tare da bayyana aikin sake ginawa da faɗaɗa babbar hanyar tarayya ta Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora, wanda kuɗinsa ya kai naira tiriliyan 1.5, a matsayin babban ci gaba da zai bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Idris ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja, lokacin da ya jagoranci membobin Ƙungiyar Tattaunawa kan Cigaban Jihar Neja (NSDF) wajen kai ziyarar ban-girma ga gwamnan.

Ya bayyana Neja a matsayin jiha mai muhimmanci ga cigaban Nijeriya, bisa la’akari da damar da take da ita a fannin noma, matsayin ta na musamman da kuma gudunmawar da take bayarwa ga samar da wutar lantarki ta tashoshin samar da wutar lantarki na Kainji, Jebba da Shiroro.

Ministan ya yaba da yadda gwamnatin Bago ta mayar da hankali kan noma ta amfani da injina, noma na kasuwanci, bunƙasa masana’antun sarrafa amfanin gona da kuma sabunta birane. Ya ace waɗannan zuba jari na kafa tubalin sauya fasalin jihar.

Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da aikin sake ginawa da faɗaɗa babbar hanyar tarayya ta Lambata–Bida–Mokwa–Makera–Kontagora, inda aka tsara gudanar da bikin aza harsashin aikin a ranar 13 ga Oktoba, 2026, a Bida.

Idris ya ce aikin zai inganta hanyoyin shiga al’ummomin manoma, haɗa kasuwanni da cibiyoyin masana’antu, tare da sauƙaƙa jigilar amfanin gona da sauran kayayyaki.

Ya ce: “Wannan wani gagarumin aiki ne a ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri na noma da kasuwanci a Nijeriya.”

Gwamna Bago ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa jihar ta hanyar ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa na tarayya, tallafin kuɗaɗen raya ƙasa da kuma naɗa ’yan jihar a muƙaman hukumomin tarayya.

Ya ce aikin hanyar zai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, bunƙasa noma da kuma inganta harkokin kasuwanci a faɗin jihar.

Idris ya kuma jajanta wa Gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ibtila’o’i da ƙalubalen tsaro na baya-bayan nan, tare da amincewa da ƙoƙarin da gwamnatocin tarayya da jiha da hukumomin tsaro suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyi.









 

No comments