Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

2027: Arewa Ta Tsakiya Ta Tashi Tsaye Domin Tinubu Yayin Da 'Yan APC Suka Yi Kwambar Goyon Baya A Lafiya

A ranar Asabar ne yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna gagarumin haɗin kan siyasa da gangamin wayar da kan al’umma, yayin da Ƙungiyar Tattara Ƙar...

A ranar Asabar ne yankin Arewa ta Tsakiya ya nuna gagarumin haɗin kan siyasa da gangamin wayar da kan al’umma, yayin da Ƙungiyar Tattara Ƙarfin Al’umma ta Arewa ta Tsakiya domin Tinubu da Shettima 2027 ta gudanar da babban gangami a dandalin Lafia Square, da ke garin Lafiya a Jihar Nasarawa.

Gangamin ya samu halartar ɗimbin magoya bayan APC, 'ya'yan jam’iyya, shugabannin al’umma, mata, matasa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa daga dukkan jihohi shida na yankin.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, shi ne ya karɓi baƙuncin taron, wanda ya haɗa da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodimma; da sauran manyan shugabannin ƙasa da na yankin, domin nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa, Kashim Shettima, a shekarar 2027.

Haka kuma, gwamnonin jihohin Neja, Binuwai, Filato, Kogi da Kwara sun halarci taron tare da gwamnan jihar da ta karɓi baƙuncin taron, wato Nasarawa. Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Alhaji Mohammed Idris Malagi, da Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Suleiman, tare da wasu ministoci.

Uwargidan Shugaban Ƙasa ta samu rakiyar matan gwamnonin jihohi shida na Arewa ta Tsakiya, abin da ya jaddada muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen tattara magoya baya da kuma ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙungiyoyin siyasar mata domin goyon bayan takarar Tinubu da Shettima.

Daga manyan hanyoyin da suka doshi dandalin Lafia Square zuwa wurin gudanar da gangamin, magoya bayan jam’iyyar sun fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su, suna kaɗa tutocin jam’iyya, ɗauke da kwalaye da allunan rubuce-rubuce, rera waƙoƙin nuna haɗin kai da kuma kirari na goyon bayan Tinubu.

Yawan jama’ar da suka halarta, tare da bayyanar manyan shugabannin siyasa daga sassan yankin, sun mayar da garin Lafiya cibiyar gangamin siyasa, tare da sanya taron ya zama muhimmin mataki a ƙoƙarin neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu a Arewa ta Tsakiya a shekarar 2027.

Da take jawabi ga ɗimbin mahalarta taron, Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana farin cikin ta da sake ziyartar Jihar Nasarawa, tare da yaba wa masu shirya taron bisa haɗa irin wannan gagarumin taro da ya tattaro shugabannin siyasa da magoya baya daga jihohi shida na Arewa ta Tsakiya.

Ta keɓance da yaba wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, wanda shi ne babban majiɓincin Ƙungiyar Tattara Ƙarfin Al’umma ta Arewa ta Tsakiya, bisa jagorancin sa da jajircewar sa wajen haɗa kan masu ruwa da tsaki.

Ta kuma yaba wa Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, bisa rawar da ya taka wajen shirya gangamin domin ƙara ƙarfafa yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaban Ƙasa.

Ta bayyana cewa mata a faɗin ƙasar nan sun fara haɗa ƙarfi da tsara ayyukan su na siyasa ƙarƙashin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Mata ta APC, da nufin tattara ƙoƙarin su wuri guda domin samar da ingantaccen dandali na haɗin gwiwa don sake zaɓen Shugaba Tinubu.

A cewar ta, wannan mataki ya nuna ƙudirin matan APC na yin aiki tare, isa gidaje da al’ummomi, tattaunawa da masu zaɓe da kuma wayar da kan su kan manufofi da nasarorin gwamnatin cikin ingantacciyar hanya.

Da take tsokaci kan jawabin Shugaban Ƙasa na ranar samun ’yancin kai, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana cewa gwamnati ta aiwatar da manyan sauye-sauye a muhimman sassan tattalin arziki, kuma yanzu lokaci ya yi da ƙasar za ta ƙarfafa waɗannan sauye-sauye domin su haifar da wadata da inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Ta kuma yi nuni da ayyukan raya ababen more rayuwa da ake gudanarwa a jihohi daban-daban, da kulawar gwamnati ga harkokin lafiya, musamman lafiyar mata masu juna biyu da walwalar su, da kuma muhimmancin shirye-shiryen tallafa wa ilimi, ciki har da lamunin karatu da Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND) ke bayarwa ga ɗalibai.

Ta jaddada cewa babban burin gwamnatin shi ne gina tattalin arziki mai ƙarfi, faɗaɗa damarmaki da samar da kyakkyawar Nijeriya wadda ’yan ƙasa za su iya sa ran samun makoma mai aminci da wadata.

A nasa jawabin, Shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe, ya taya masu shirya gangamin murna, yana mai bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin manyan gangamin siyasa mafi nasara da tasiri wajen nuna goyon baya ga sake zaɓen Tinubu.

Farfesa Yilwatda ya yaba wa Ƙungiyar Tattara Ƙarfin Al’umma ta Arewa ta Tsakiya bisa haɗa shugabanni, tsarin jam’iyya da talakawa daga sassan yankin domin cimma manufa guda ta siyasa.

Ya kuma yi yabo na musamman ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, da gwamnan da ya karɓi baƙuncin taron da sauran masu ruwa da tsaki waɗanda haɗin gwiwar su ya ba da damar gudanar da taron.

Shugaban na APC ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu saboda jajircewar sa wajen sanya Nijeriya a kan turbar cigaba mai ɗorewa, aiwatar da sauye-sauye masu wahala amma wajibi, da kuma aza harsashin tattalin arziki mai ƙarfi da wadata.

Farfesa Yilwatda ya ƙara da cewa Arewa ta Tsakiya ta samu kulawa da ayyukan cigaba masu muhimmanci daga Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Tinubu, yana mai cewa akwai dalilai masu ƙarfi da ya kamata su sa yankin ya ƙara ƙarfafa alaƙar sa da gwamnatin.

Ya yi kira ga al’ummar Arewa ta Tsakiya da su rama ƙoƙarin da Shugaban Ƙasa yake yi wa yankin ta hanyar fitowa ƙwan su da ƙwarƙwatar su domin zaɓen Tinubu da Shettima a zaɓen Janairu 2027, tare da goyon bayan sauran ’yan takarar APC a matakan gwamnati daban-daban.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodimma, ya yaba wa masu shirya taron bisa haɗa shugabannin siyasa da magoya baya daga sassan Arewa ta Tsakiya, da kuma samar da dandali na ƙara ƙarfafa goyon baya ga gwamnatin Sabuwar  Fata.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar sun zama wajibi domin sake tsara tattalin arzikin ƙasar nan zuwa turbar cigaba mai ɗorewa. 

Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi la’akari da manyan manufofin gwamnatin yayin da ƙasar ke fuskantar sauye-sauyen tattalin arziki.

Sanata Uzodimma ya yi kira ga al’ummar Arewa ta Tsakiya da su fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su a zaɓen Janairu 2027 domin zaɓen Shugaba Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima da sauran ’yan takarar APC.

Gwamnonin da sauran shugabannin siyasar da suka yi jawabi a gangamin sun bayyana goyon bayan su ga manufofin sauye-sauyen gwamnatin, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi wajen bunƙasa ababen more rayuwa, tattalin arziki, tsaro da walwalar al’umma.

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, wanda ya karɓi baƙuncin taron, ya yi maraba da Uwargidan Shugaban Ƙasa da sauran manyan baƙi zuwa jihar, tare da yaba wa al’ummar Arewa ta Tsakiya bisa fitowa da suka yi a ɗimbin yawa.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai, ingantaccen tsarin siyasa da ci gaba da hulɗa da ’yan ƙasa yayin da yankin ke shirin tunkarar zaɓen shekarar 2027.










 

No comments