Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara zurfafa hulɗar sa ta fannin kuɗi da hukumomi da ƙasashen Nahiyar Asiya, baya...
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara zurfafa hulɗar sa ta fannin kuɗi da hukumomi da ƙasashen Nahiyar Asiya, bayan gudanar da jerin manyan tarurruka a Singapore.
Tarurrukan dai sun haɗa da tattaunawa da Hukumar Kuɗi ta Singapore (MAS), tare da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wato MoU, kan ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya jagoranci waɗannan tattaunawa a kan hanyar sa ta zuwa Bangkok domin halartar Taron Shekara-shekara na Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.
CBN dai na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar Nijeriya da kasuwannin kuɗi na nahiyar Asiya da kuma jawo ƙarin jarin da zai daɗe yana tasiri a ƙasar nan.
CBN ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Global Finance & Technology Network (GFTN), wadda ta samar da tsarin haɗin gwiwa kan ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi, tare da haɗa cibiyoyi da tsarin bunƙasa sabbin dabaru da fasahohi a Nijeriya da Singapore.
A cewar CBN, waɗannan hulɗoɗi na daga cikin ƙoƙarin mayar da sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren kuɗi na Nijeriya zuwa ingantattun haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, faɗaɗa kasuwannin kuɗi da samar da hanyoyi masu amfani don zuba jari, kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kuɗi.
A yayin tattaunawar sa da MAS, tawagar CBN ta yi musayar ra'ayoyi kan bunƙasa ɓangaren kuɗi, dokoki da ƙa'idojin gudanar da harkokin kuɗi, haɗin kan kasuwanni da sabbin fasahohi.
Haka kuma, sun gano wasu fannoni da za su ci gaba da haɗin gwiwa a kai tsakanin hukumomin biyu.
A wani taron tattaunawa mai taken Haɗa Kasuwannin Kuɗi Tsakanin Nijeriya da Asiya, wanda CBN ya shirya tare da haɗin gwiwar J.P. Morgan, Nigerian Exchange Group (NGX) da FMDQ Group, Cardoso ya bayyana burin Nijeriya na gina kasuwannin kuɗi masu zurfi, masu yawan hada-hadar kuɗi, kuma masu kyakkyawar alaƙa da kasuwannin duniya.
An gudanar da taron ne a ofisoshin J.P. Morgan da ke Singapore, ƙarƙashin jagorancin Dapo Olagunji, Manajan Daraktan J.P. Morgan mai kula da Yammacin Afirka. Taron ya haɗa masu zuba jari, cibiyoyin kuɗi, 'yan kasuwa da kuma 'yan Nijeriya da ke zaune da aiki a sassa daban-daban na nahiyar Asiya.
Cardoso ya ce an tsara sauye-sauyen da Nijeriya ta aiwatar a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ne domin kawar da gurɓatattun hanyoyin gudanar da kasuwa, inganta gaskiya da bayyana bayanai, da kuma dawo da amincewa da ƙa'idojin da ke jagorantar masu shiga harkokin kuɗaɗe.
Ya ce: “Babban abin da zai nuna nasarar gyare-gyare ba wai ko za ka iya jawo jari sau ɗaya ba ne; a'a, shi ne ko za ka samar da amincewar da za ta sa jarin ya zauna, ya dawo, kuma ya ci gaba da bunƙasa.”
Gwamnan ya bayyana cewa ingantacciyar manufar kuɗi, ƙarfafa tsarin shugabanci da gudanarwa, inganta yadda kasuwanni ke aiki, da samar da ƙa'idoji masu tabbas, duk suna da muhimmanci wajen jawo jarin cikin gida da na ƙasashen waje wanda zai daɗe yana aiki.
Ya ƙara da cewa daidaituwar kasuwannin kuɗi ya kamata ta zama tubalin ƙara shigar masu zuba jari na dogon lokaci, ƙarfafa kayayyakin more rayuwa da tsarin gudanar da kasuwannin kuɗi, da kuma zurfafa alaƙa da kasuwannin kuɗi na duniya.
Taron ya kuma tattauna kan tafarkin gyare-gyaren da Nijeriya ke bi, samar da jari, dawo da amincewa da kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma kayayyakin more rayuwa da ake buƙata domin tabbatar da ci gaba da shigar masu zuba jari na ƙasashen duniya.
Wani zaman tattaunawa da Gbolahan Taiwo, Babban Masanin Tattalin Arziƙi na J.P. Morgan mai kula da Afirka, ya jagoranta, ya ƙunshi Temi Popoola, Babban Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa na NGX Group; Zeal Akaraiwe, Babban Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa na FMDQ Group; Aderinola Shonekan, Daraktan Ciniki da Canjin Kuɗi a CBN; da Olumayokun Ajibade, Mai Ba Gwamnan CBN Shawara na Musamman kan Kasuwannin Kuɗi da Manufofin Tattalin Arziƙi.
Cardoso ya ce hulɗar Nijeriya da Asiya ba ta taƙaita ga jawo kuɗaɗen zuba jari kawai ba. A maimakon haka, ana kuma son gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin cibiyoyin kuɗi, kasuwanni, 'yan kasuwa da kuma 'yan Nijeriya da ke zaune a yankin.
Ya bayyana cewa akwai damar ƙarfafa alaƙa tsakanin bankunan Nijeriya da na Asiya, da kuma cibiyoyin kasuwannin kuɗi na ɓangarorin biyu. Haka kuma, akwai damar samar da hanyoyin biyan kuɗi da daidaita hada-hadar kuɗi cikin sauƙi da inganci, tare da ƙara shigar 'yan Najeriya da ke zaune da aiki a Asiya cikin harkokin kasuwannin kuɗi.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da fasahar kuɗi da basirar na'ura mai kwakwalwa (AI) ke takawa wajen inganta ayyukan kuɗi, ƙarfafa hanyoyin tantancewa da kula da haɗurra, bunƙasa shigar jama'a cikin harkokin kuɗi, da inganta ƙarfin hukumomin sa-ido da tsara dokoki.
Waɗannan tarurruka da aka gudanar a Singapore na daga cikin babban shirin CBN na gudanar da hulɗa da hukumomi da kasuwannin kuɗi a faɗin Asiya. Ana kuma sa ran gudanar da ƙarin tarurruka a birnin Beijing na ƙasar Sin.

No comments