* Uwargida Oluremi Za Ta Jagoranci Gangamin Ƙungiyar Tattara Goyon Baya a Ƙananan Hukumomi a Arewa ta Tsakiya ta bayyana shirin ta na gudana...
Ƙungiyar Tattara Goyon Baya a Ƙananan Hukumomi a Arewa ta Tsakiya ta bayyana shirin ta na gudanar da wani babban gangami a garin Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, ranar Asabar mai zuwa domin nuna cikakken goyon bayan yankin ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa, Sanata Kashim Shettima, a babban zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, shi ne zai karɓi baƙuncin gangamin, yayin da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta kasance babbar baƙuwa ta musamman.
Sanarwar ta biyo bayan wani babban taro na jiga-jigan jam'iyyar APC na yankin Arewa ta Tsakiya wanda aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam'iyyar na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; gwamnoni da mataimakan su daga yankin; ministoci; 'yan Majalisar Tarayya; da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron, sai da Farfesa Yilwatda ya miƙa ta'aziyyar sa ga iyalan waɗanda suka rasu a haɗarin jirgin saman Rundunar Sojin Saman Nijeriya da ya faru kwanan nan a Jihar Ondo, da kuma iyalan waɗanda suka rasu a wani mummunan lamari da ya shafi harkar haƙar ma'adinai a Jihar Neja.
Ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan mamatan da al'ummomin da lamarin ya shafa, yana mai bayyana waɗannan al'amurra a matsayin babban rashi mai raɗaɗi.
Da yake magana kan sakamakon taron, Shugaban na APC ya bayyana cewa gwamnoni, ministoci, 'yan majalisa da sauran jiga-jigan siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya sun amince baki ɗaya su tattara dukkanin tsare-tsaren siyasa da magoya bayan su domin tabbatar da nasarar gangamin.
Ya bayyana taron da ake shirin gudanarwa a matsayin “uban dukkan gangamin siyasa”, inda ya ce babbar manufar sa ita ce nuna haɗin kan yankin wajen goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu da Mataimakin sa, Shettima, a shekarar 2027.
A cewar Shugaban na APC, taron ya nuna irin ƙudirin da jiga-jigan siyasar da suka halarta suke da shi na haɗa kai wajen gudanar da ayyukan su da kuma ƙarfafa hulɗa da jama'a a matakin tushe domin tallafa wa takarar Tinubu da Shettima.
Taron ya yaba wa jagorancin Sanata Akume bisa ƙoƙarin sa na haɗa jiga-jigan siyasa daga sassa daban-daban na yankin Arewa ta Tsakiya.
Haka kuma, mahalarta taron sun yaba wa Gwamna Sule bisa amincewar sa ta karɓar baƙuncin gangamin a Jihar Nasarawa.
Jiga-jigan siyasar sun kuma nuna farin cikin su da shigar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, cikin waɗanda za su halarci taron a matsayin babbar baƙuwa ta musamman.
Sun duba shirye-shiryen halartar taron da shugabannin jam'iyyar, ƙungiyoyin mata da matasa, ƙungiyoyin jama'a na matakin tushe da sauran magoya baya daga jihohi shida na yankin Arewa ta Tsakiya da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An kammala taron ne tare da sake jaddada matsayar mahalarta baki ɗaya kan jajircewar su ta tabbatar da nasarar gudanar da gangamin siyasar a Lafiya, da kuma goyon bayan sake zaɓen Tinubu da Shettima.






No comments