Daga Ashafa Murnai Barkiya Sabon binciken baya-bayan nan da Babban Banki Nijeriya (CBN) ya ya fitar, ya nuna yadda magidanta a Nijeriya suka...
Sabon binciken baya-bayan nan da Babban Banki Nijeriya (CBN) ya ya fitar, ya nuna yadda magidanta a Nijeriya suka fi mayar da hankali kan sayen abinci fiye da zuba jari da sayen gidaje a cikin watan Satumba.
Wannan bincike dai na nuni da cewa hauhawar farashin kayayyaki da raunin tattalin arzikin magidanta na ci gaba da yin tasiri kan yadda suke kashe kudaden su. Haka dai Binciken Hasashen Iyalan Nijeriya na watan Satumba na shekarar 2026, wanda CBN ya gudanar ya tabbatar.
Binciken ya nuna cewa abinci ne ya kasance abin da iyalai suka fi ba muhimmanci wajen kashe kuɗi a watan Satumba, sai sufuri, sauran kayan amfanin gida, harkokin ilimi, wutar lantarki da ruwa.
CBN ya ce ana kuma sa ran abinci, sufuri, kayan amfanin gida da ilimi za su ci gaba da kasancewa manyan abubuwan da iyalai za su fi kashe kuɗi a kan su cikin watanni uku zuwa shida masu zuwa.
Abinci ke kan gaba, inda ya samu ma’aunin kashe kuɗi har maki 56.1 a watan Satumba, wanda ya yi nisa a gaban sauran kayan amfanin gida da suka samu maki 28.3, ilimi 27.6, wutar lantarki da ruwa 17.1, yayin da harkar sadarwa ta samu maki 9.3.
An yi hasashen cewa ma’aunin kashe kuɗin abinci zai kasance maki 54.7 cikin watanni uku masu zuwa, sannan ya kai 54.9 cikin watanni shida nan gaba.
Wannan na nuna cewa abubuwan da suka shafi muhimman buƙatun yau da kullum za su ci gaba da kasancewa a tsakiyar kasafin kuɗin iyalai.
Sai dai, iyalai sun nuna ƙarancin sha’awar ɗaukar manyan nauyin kuɗi. Ma’aunin ra’ayin zuba jari ya kasance maki -50.7 a watan da ake nazari, yayin da sayen kayan amfani masu ɗorewa ya kasance maki -49.5.
Sayen motocin haya ya samu maki -67.3, yayin da sayen gidaje ya kasance mafi rauni, da maki -68.2
A cikin watanni shida masu zuwa kuma, buƙatar zuba jari za ta kasance maki -60.8, sayen gidaje -62.8, yayin da sayen motocin haya ya kasance -43.4.
Wannan rashin son karkatar da kuɗin shiga zuwa kadarori da manyan sayayya ya zo ne a daidai lokacin da amincewar masu amfani da kayayyaki ke ci gaba da raguwa.

No comments