Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babban Kwamandan ISWAP, Abdussamad Ohida, Ya Baƙunci Lahira A Ondo

Wata rundunar haɗin gwiwa da ta ƙunshi sojojin Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya, jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Ƙasa (DSS) da jami’an...




Wata rundunar haɗin gwiwa da ta ƙunshi sojojin Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya, jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Ƙasa (DSS) da jami’an Cibiyar Tsaron Yammacin Nijeriya da aka fi sani da Amotekun, ta kashe wani babban kwamandan ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), Abdussamad Ohida, a wani dajin Owo da ke Jihar Ondo.

Majiyoyin tsaro sun ce Ohida, wanda aka fi sani da Anwar, yana shirin kai manyan hare-haren ta’addanci a wasu jihohin kudancin Nijeriya kafin jami’an tsaron su kai samame ba zato ba tsammani a maboyar ’yan ƙungiyar da ke cikin dajin a ƙarshen makon da ya gabata.

Majiyoyin sun ce an kashe Ohida tare da wasu mambobin ƙungiyar ta’addancin yayin farmakin.

A cewar majiyoyin, Ohida ya taɓa zama mataimakin shugaban ayyukan ISWAP a yankin tsakiyar Nijeriya, Abu Ikrimah, wanda aka fi sani da Abu Uwais. Hukumar DSS ta kama Ikrimah a shekarar 2023.

Bayan kama Ikrimah, majiyoyin sun ce Ohida ya karɓi ragamar jagorantar ayyukan ISWAP a wasu sassan Arewa ta Tsakiya da kudancin ƙasar, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa, haɗa kai da kuma aiwatar da hare-haren ta’addanci.

Majiyoyin sun ƙara da cewa, bayan yi wa Abu Uwais tambayoyi, DSS ta samu sahihan bayanan sirri kan shirin Ohida na kai hare-hare kan fararen hula a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

“Shirin shi ne a kai wa fararen hula hari a lokacin bukukuwan, daga bisani kuma a tarwatsa babban zaɓen 2027. Abokan hulɗarmu na leƙen asiri daga Birtaniya sun tabbatar da waɗannan bayanan, kuma sun taimaka wajen aikin da ya kai ga kawar da shi,” in ji wata majiya.

Majiyar ta ce Ohida ne ya shirya tare da aiwatar da harin da aka kai ranar 31 ga Disamba, 2025, kan Ofishin ’Yan Sandan Ipele da ke Owo, Jihar Ondo, inda aka kwashe bindigogi kirar AK-47 guda takwas kafin daga bisani a tarwatsa ofishin da wani abin fashewa.

Ta kuma danganta Ohida da harin da aka kai ranar 28 ga Yuli, 2022, kan shingen binciken sojoji da ke kan hanyar Suleja zuwa Zuba a Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji, jami’an tsaro da fararen hula.

Haka kuma, majiyar ta zargi Ohida da hannu wajen harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja a ranar 11 ga Yuli, 2022; harin da aka kai Ofishin ’Yan Sandan Ogaminana da ke Ƙaramar Hukumar Adavi a Jihar Kogi a ranar 23 ga Afrilu, 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar ’yan sanda biyar; da kuma harin ranar 7 ga Fabrairu, 2022 kan Ofishin ’Yan Sandan Yankin Okene.

“’Yan ta’addan sun shirya tare da aiwatar da harin ranar 24 ga Disamba, 2020 kan wani shingen binciken Rundunar Sojin Ruwa da ke Okene, Jihar Kogi, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an sojin ruwa biyu, ban da sauran hare-haren da ya kai a sassa daban-daban na ƙasar,” in ji majiyar.

Majiyar ta ce kashe Ohida ya kawo babban cikas ga tsarin shugabanci na ISWAP, hanyoyin gudanar da ayyukanta da kuma ƙoƙarinta na faɗaɗa ayyukan ƙungiyar a yankunan Arewa ta Tsakiya da kudancin Nijeriya.

“Mai yiwuwa ba za mu fahimci girman abin nan take ba, amma kashe Abdussamad Ohida babban cikas ne ga shugabancin ISWAP, hanyoyin gudanar da ayyukanta da kuma ƙoƙarinta na faɗaɗa ayyukanta a tsakiyar Nijeriya da kudancin ƙasar,” in ji majiyar.

Ta ƙara da cewa kisan Ohida, wanda ya zo ’yan watanni bayan kashe shugaban ISIS, Abu Bilal al-Minuki, babban koma-baya ne ga ƙoƙarin ISWAP na faɗaɗa ayyukanta a Nijeriya, tare da nuna yadda hukumomin tsaron ƙasar ke ƙara samun ƙwarewa wajen dakile ayyukan ƙungiyoyin ta’addanci.

No comments