Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Biyan Kuɗin Fansa, Tamkar Taimaka Wa 'Yan Ta'adda Ne A Ta'addancin Su — Gwamnan Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayinsa na ƙin amincewa da biyan kuɗin fansa ko shiga sulhu da masu garkuwa da mutane...

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada matsayinsa na ƙin amincewa da biyan kuɗin fansa ko shiga sulhu da masu garkuwa da mutane da ke addabar al’ummar jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce biyan kuɗin fansa ga masu aikata laifuka na ƙarfafa musu gwiwa ne tare da ba su damar ci gaba da aikata ta’addanci.

Ya kuma ce abubuwan da suka faru a baya sun nuna cewa tattaunawa da ’yan bindiga ba ta haifar da wani sakamako mai kyau ba.

Gwamna Lawal ya bayyana cewa, matsayinsa kan batun ƙin biyan fansa ya samo asali ne daga irin gwagwarmayar da iyalinsa suka fuskanta a lokacin da aka sace ’yan uwansa, Yusuf da Amba, a shekarar 2025.

“Ka sani, akwai wasu tsauraran matakai da dole shugaba ya ɗauka idan aka zo batun iyalinsa. Na bayyana matsayina a fili, amma idan wani yana ganin akasin haka, yana da ’yancin ya je ya biya kuɗin ya dawo da Yusuf da Amba,” in ji gwamnan.

Ya ce ’yan garkuwar sun ci gaba da neman kuɗi, amma daga ƙarshe suka gaji bayan sun fahimci cewa ba zai biya su ba.

“Daga ƙarshe sun gaji, kuma abin da suka nema na ƙarshe, kamar yadda nake tunawa, shi ne katin recharge na Naira 150,000. Ko wannan ma na ce ba zan biya ba. Wani daga cikin iyalin ya kamata ya yi hakan, saboda na yi alkawarin cewa ba zan taɓa saka ko kwabo cikin hannun mai laifi ba,” in ji shi.

Matsayar gwamnan ta zo ne a daidai lokacin da Jihar Zamfara ke ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga da masu ta’addanci, lamarin da ya jefa al’ummomi da dama cikin fargaba tare da tilasta wa hukumomin tsaro ƙara kaimi wajen dakile hare-haren.

A watan Janairu, wasu ’yan bindiga da ake zargi sun yi wa jami’an tsaro kwanton bauna a yankin Kwatarkwashi da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu, inda aka kashe sojoji biyar da wani Sufeto na ’Yan Sanda.

A watan Fabrairu kuma, an kashe mutane 30 tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka.

Haka kuma, an tabbatar da mutuwar wasu mutane 11 a wani harin da aka kai a garin Ware, da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.

A watan Afrilu, ’yan bindigar da ake zargi sun kai hari al’ummar Kurfa da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin da ba a bayyana adadinsu ba.

Kwanaki kaɗan bayan harin, jami’an tsaro sun ce sun kashe sama da ’yan bindiga 30 da ake zargi, a wani samamen ramuwar gayya da suka gudanar a yankin Tsafe.

A watan Mayu, fashewar wani bam da aka dasa a hanya ya kashe mutane shida tare da jikkata wasu shida a kan hanyar Bagega zuwa Anka. A wani makamancin lamarin kuma, ’yan ta’adda da ake zargi sun yi wa matafiya kwanton bauna a hanyar Magami zuwa Dansadau, inda ake fargabar cewa an kashe tare da yin awon gaba da wasu daga cikinsu.

Hare-haren dai sun ci gaba a watannin Yuni da Yuli, inda aka sace mutane 39 a lokacin da suke gudanar da wani aikin sulhu a Maradun, yayin da aka kuma yi awon gaba da ɗalibai bakwai a Kaura Namoda.

A watan Yuli, ’yan ta’adda sun kai hari gidan shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu, inda suka yi awon gaba da shi. Harin ya kuma yi sanadin mutuwar ’yan sanda biyu, wani jami’in sa-kai da kuma wani farar hula.

Har zuwa watan Satumba, jami’an soji sun ceto matafiya 41 da aka yi garkuwa da su bayan motar kasuwanci da suke ciki ta lalace a kan hanyar Tsafe zuwa Funtua.

Wannan lamari ya sake jaddada irin ƙalubalen tsaro da ke fuskantar manyan hanyoyin Jihar Zamfara, musamman waɗanda ke haɗa ƙananan hukumomi da garuruwa masu muhimmanci.

Sai dai Gwamna Lawal ya ce gwamnatinsa na ci gaba da ɗaukar matakan inganta martanin jami’an tsaro ga hare-hare, musamman a yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro kamar Tsafe.

Ya ce manufar gwamnatin ita ce rage lokacin da jami’an tsaro ke ɗauka wajen mayar da martani ga hare-hare, tare da ƙarfafa tsarin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
 

No comments