Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun kashe fiye da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laif...
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun kashe fiye da ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka 102, sun kama mutum 345 da ake zargi da aikata laifuffuka, tare da kuɓutar da mutane 393 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan cikin watan Yuli.
Rundunar ta kuma ce ta ƙwato bindigogi 59 da harsasai 1,811, yayin da ‘yan ta’adda 57 tare da iyalansu suka miƙa wuya ga dakarun soji a hare-haren da aka gudanar a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar.
Daraktan Yaɗa Labaran Ayyukan Tsaro na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na wata-wata da aka gudanar a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.
A cewarsa, an samu waɗannan nasarori ne sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan maɓoyar ‘yan ta’adda, amfani da bayanan sirri, ayyukan ceto da kuma haɗin gwiwar jami’an tsaro da ƙungiyoyin al’umma.
Ya ƙara da cewa dakarun soji sun ci gaba da kare manyan hanyoyin sufuri, tituna da layukan dogo domin tabbatar da zirga-zirgar jama'a, kayayyaki da ayyukan kasuwanci cikin aminci.
A yankin Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 54, sun kama mutum 102 tare da kuɓutar da mutane 102 da aka yi garkuwa da su, yayin da mayaƙa 57 tare da iyalansu suka miƙa wuya.
Rundunar ta ce ta yi wa Boko Haram da ISWAP mummunan rauni bayan kashe wani babban kwamandan ƙungiyar kuma shugaban yaɗa farfagandarta, Abu Salim al-Barnawi, a wani farmaki da aka kai a Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Haka kuma, wani babban jami'in kula da kuɗaɗen ISWAP ya miƙa wuya a hanyar Gamboru-Wulgo, inda ya mika bindigar AK-47, mujallu huɗu, harsasai 101, babur da kuɗi.
A yankin Arewa maso Yamma, dakarun Operation Fansan Yamma sun kuɓutar da mutum 191 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ‘yan ta’adda 33 tare da kama wasu 66 a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi da Zamfara.
An kuma ƙwato makamai da alburusai tare da ceto fararen hula da dama daga sansanonin ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
Daga cikin waɗanda aka ceto akwai Shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, Dakta Aminu Yusuf, tare da iyalansa da kuma wasu da aka sace a hare-haren da aka kai a Zamfara da Sakkwato.
A yankin Arewa ta Tsakiya, dakarun Operation Savannah Shield, Operation Enduring Peace da Operation Whirl Stroke sun samu gagarumar nasara kan masu garkuwa da mutane, ‘yan ta’adda, masu safarar makamai da ƙungiyoyin masu tayar da tarzoma.
Operation Savannah Shield ta kashe ‘yan ta’adda takwas, ta kama mutum 18 tare da ceto mutum 11.
Operation Enduring Peace kuwa ta kashe ‘yan ta’adda biyu, ta kama mutum 60 tare da kuɓutar da mutum 18.
Operation Whirl Stroke kuma ta kashe ‘yan ta’adda biyar, ta kama mutum 70 tare da ceto mutum 24 a jihohin Benue, Kogi, Nasarawa da Taraba.
Rundunar ta kuma kashe wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda mai suna Puuga a Benue, tare da ceto mutane da dama, ciki har da shugaban makaranta, wani jami’in Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Makarantun Sakandare (NECO) da ɗalibai biyu da aka sace daga cibiyar rubuta jarabawa a Jihar Kogi.
A yankin Kudu maso Kudu, dakarun Operation Delta Safe sun kama mutum uku da ake zargi da ta’addanci, sun ceto fararen hula 37 tare da rusa matatun ɗanyen mai ba bisa ka’ida ba guda 18.
Sun kuma ƙwato fiye da lita 250,500 na man fetur da sauran kayayyakin mai, yayin da suka dakile ayyukan masu garkuwa da mutane, fashin teku da satar ɗanyen mai a yankin Neja Delta.
A Kudu maso Gabas kuwa, dakarun Operation Udo Ka sun kama mutum 26 da ake zargi da aikata laifuffuka, tare da kuɓutar da fararen hula 10 a hare-haren da suka kai kan masu rajin ballewa, masu safarar makamai, masu garkuwa da mutane da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa a jihohin Abia, Anambra, Enugu, Imo da Rivers.
An kuma ƙwato bindigogi da sauran makamai daga maɓoyar masu laifin.
Manjo Janar Onoja ya ce rundunar sojin sama ta taimaka wajen kai hare-haren da suka kashe ‘yan ta’adda a yankin Kontagora na Jihar Neja ranar 25 ga Yuli, bayan bayanan sirri sun tabbatar da shirin kai hari.
Ya ƙara da cewa wani farmakin sama da aka kai ranar 6 ga Yuli ya bai wa mutane tara da aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Mariga damar tserewa.
Baya ga ayyukan yaƙi, rundunar ta ƙara ƙaimi wajen ayyukan hulɗa da al’umma, ciki har da zaman sulhu, ayyukan kiwon lafiya, gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, makarantu, dakunan taro da sauran ayyukan raya ƙasa.
A Borno, dakarun sun taimaka wajen shawo kan ɓarkewar cutar kwalara a Cross Kauwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, tare da haɗin gwiwar hukumomin lafiya.
Onoja ya ce nasarorin watan Yuli sun nuna ƙudirin rundunar wajen raunana ƙarfin ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuffuka, domin samar da yanayin da zai ba da damar bunƙasar tattalin arziki da ci gaba.
Ya kuma yabawa dakarun soji da sauran jami’an tsaro bisa rawar da suka taka wajen kuɓutar da ɗalibai 44 da malamansu da aka sace a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
A ƙarshe, ya ce Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, ya yaba wa ƙwarin guiwar dakarun soji, tare da sake jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyi da kuma kawo ƙarshen ta’addanci, garkuwa da mutane, masu rajin ballewa da sauran miyagun laifuffuka a faɗin ƙasar nan.
Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya su ɗauki tsaron ƙasa a matsayin alhakin kowa da kowa, tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri domin taimaka wa ayyukansu.
.jpg)
No comments