Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda 'Yan Bindiga Suka Dira Shagon PoS, Suka Kashe Mutum 3 A Kaduna

Aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan ...




Aƙalla mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan wani shagon POS a ƙauyen Galadimawa da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata, 4 ga Agustan 2026.

Majiyoyin yankin sun bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne a kan babura biyu ɗauke da bindigogin AK-47, inda suka nufi shagon POS kai tsaye kafin su buɗe wa mutanen da ke wurin wuta.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa mutane biyar ne suka samu raunukan harbi a harin.

A cewarsa, uku daga cikinsu sun mutu nan take, yayin da sauran biyun suka jikkata kafin maharan su kwashe kuɗi masu yawa daga shagon tare da tserewa.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin ci gaba da kula da lafiyarsu.

An bayyana sunayen waɗanda suka rasu da Alhaji Hassan Abdullahi, Yakubu Mu'azu da Magaji Sarauta.

Yayin da waɗanda ke karɓar magani saboda raunukan harbi su ne Aliyu Rufai da Umar Mohammed.

Bayan harin, al'ummar Galadimawa sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta ƙara tura jami'an tsaro, musamman sojoji, domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Wani jagoran al'umma, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce hare-haren 'yan bindiga da ake kai wa ƙauyukan da ke makwabtaka da Galadimawa sun tilasta wa mazauna wuraren tserewa zuwa garin, lamarin da ya ƙara jefa yankin cikin haɗarin hare-hare.

No comments