Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RAHOTON CBN: Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Ƙara Bunƙasa Da Kashi 3.87 Cikin Ɗari A 2025

Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar, wato GDP ya ƙara bunƙasa da ka...

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar, wato GDP ya ƙara bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a shekarar 2025.

Wannan ƙari da aka samu kuwa ya fi na kashi 3.38 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2024.

CBN ya bayyana hakan ne a cikin rahoton sa na shekara ta 2025 da aka fitar kwanan nan.

A rahoton na CBN, wannan bunƙasa mai faɗi ta samo asali ne daga ci gaba da aiwatar da jerin sauye-sauyen tattalin arziki a muhimman fannoni, tare da sake fasalin yadda ake ƙididdige tattalin arzikin ƙasa domin haɗa sabbin ƙananan sassa da suka fara taka muhimmiyar rawa.

Bankin ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 15.15 cikin ɗari a watan Disamba na 2025, watau daga kashi 34.80 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2024.

Ya bayyana cewa hakan ya samu ne sakamakon haɗakar tsauraran matakan manufofin kuɗi, daidaituwar canjin kuɗaɗen waje, da kuma sake fasalin hanyar da ake amfani da ita wajen ƙididdige Ma’aunin Farashin Kayan Masarufi, watau 'Consumer Price Index', wanda aka fi sani da CPI.

“Sabuwar hanyar ƙididdigar ta sabunta nauyin abubuwan da ake la’akari da su a cikin kwandon CPI, domin ya fi nuna yadda gidaje ke kashe kuɗin su a halin yanzu.

“Haka kuma, yanayin kuɗaɗen gwamnati ya nuna alamun ingantuwa a shekarar 2025, inda kuɗaɗen shiga na Asusun Tarayya suka ƙaru da kashi 33.67 cikin ɗari, sakamakon ƙarin kuɗaɗen shiga daga fannin mai da kuma sauran fannoni waɗanda ba na mai ba.

Wannan rahoto ya ci gaba da bayyana cewa, “saboda haka, rabon kuɗaɗen da ake bai wa matakan gwamnati uku ya ƙaru, lamarin da ya ƙarfafa ɗorewar tsarin kuɗaɗen gwamnati."

CBN ya kuma ce yawan harajin da gwamnati ke tarawa idan aka kwatanta da girman tattalin arzikin ƙasa (GDP) ya ƙaru zuwa kashi 7.15 cikin ɗari a shekarar 2025, daga kashi 5.41 cikin ɗari a shekarar 2024.

Ya ce wannan ƙarin ya samo asali ne daga ƙaruwar kuɗaɗen harajin ribar man fetur, harajin ƙimar kaya (VAT), da kuma harajin kuɗaɗen shigar kamfanoni.

“Zuwa ƙarshen watan Satumba na 2025, jimillar bashin gwamnati ta kai Naira tiriliyan 153.29, wanda ya kai kashi 35.55 cikin ɗari na GDP. Duk da haka, wannan adadi yana ƙasa da iyakar kashi 60 cikin ɗari da ƙasa ta gindaya, da kuma iyakar kashi 70 cikin ɗari da ake ba da shawara ga ƙasashen da ke samun damar karɓar bashi daga kasuwannin duniya (Market-Access Countries),” inji rahoton.

CBN ya ce tattalin arzikin duniya ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali a shekarar 2025, duk da ƙalubalen rashin tabbas da suka ƙaru.

“Ko da yake bunƙasar tattalin arzikin duniya ya ci gaba da kasancewa a kashi 3.30 cikin ɗari, ci gaban bai kasance iri ɗaya ba a dukkan yankuna.

“A ƙasashen da suka ci gaba, bunƙasar tattalin arziki ta ragu zuwa kashi 1.70 cikin ɗari daga kashi 1.80 cikin ɗari, sakamakon raguwar buƙatu.

“Amma a ƙasashe masu tasowa da kuma kasuwanni masu bunƙasa (EMDEs), bunƙasar tattalin arziki ta ƙaru zuwa kashi 4.40 cikin ɗari, idan aka kwatanta da kashi 4.30 cikin ɗari a shekarar 2024, sakamakon ci gaba da aiwatar da manufofin tallafa wa tattalin arziki,” inji rahoton na CBN.

Haka kuma CBN ya ce hauhawar farashin kayayyaki a duniya ta ragu zuwa kashi 4.20 cikin ɗari, sakamakon saukar farashin makamashi da kayan abinci, da kuma tasirin tsauraran manufofin kuɗi da aka aiwatar tun da farko.

“A ƙasashen da suka ci gaba, hauhawar farashin kayayyaki ta ɗan ragu zuwa kashi 2.50 cikin ɗari, daga kashi 2.60 cikin ɗari a shekarar 2024.

“Amma a ƙasashe masu tasowa da kasuwanni masu bunƙasa, raguwar ta fi sauri, inda hauhawar farashin kayayyaki ta sauka zuwa kashi 5.20 cikin ɗari, daga kashi 7.90 cikin ɗari.

“Kasashe da dama sun rage yawan kuɗin ruwa a shekarar 2025, bayan hauhawar farashin kayayyaki ta lafa, tare da ƙoƙarin cimma manufofinsu na tattalin arziki,” inji CBN.

Har ila yau, CBN ya ce yanayin manufofin kuɗaɗen gwamnati a duniya ya ci gaba da fuskantar ƙalubale, saboda yawan bashin da ƙasashe ke ɗauke da shi da kuma ƙarin kashe kuɗaɗe a fannin tsaro.

A cewar CBN, yanayin kasuwannin kuɗi na duniya a lokacin da rahoton ya shafa ya samu tasiri daga sauye-sauyen siyasa da rikice-rikicen ƙasa da ƙasa, da kuma abubuwan da suka faru a manyan tattalin arzikin duniya.

Bankin ya ce kasuwannin hannayen jari sun kasance cikin yanayi mai kyau, abin da ke nuna ƙarfi a ribar kamfanoni da kuma sauyin hasashen manufofin tattalin arziki.

“Haka kuma, farashin kayayyaki a kasuwannin duniya ya ragu gaba ɗaya, inda matsakaicin farashin gangar ɗanyen man Bonny Light ya sauka zuwa dala 70.93 kan kowace ganga, daga dala 82.56 a shekarar 2024, sakamakon yawaitar ɗanyen mai a kasuwar duniya.”

No comments