Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, tare da mambobin Tawagar Sadarwa ta Ƙasa (National Communication Team), a yayin ziyar...
Ziyarar ta kasance wani bangare na ƙoƙarin wayar da kan jama’a tare da fito da dumbin ayyunkan cigaba da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu keyi a fili a fannoni daban daban.
Tawagar ta kunshi Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Cif Sunday Dare; Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Daidaita Manufofi, Hadiza Bala Usman; da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Hulɗa da Jama’a da Wayar da Kai, Malam Abdul’aziz Abdul’aziz, da sauran mambobin Tawagar Sadarwa ta Ƙasa, tare da manyan 'yan jarida.

No comments