Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masoyin Ɗan Takarar Gwamnan Nasarawa Ya Raba Wa Mata Injin Niƙa A Lafia

Daga Zubairu Lawal, Lafia Wani matashin ɗan siyasa, Abbas Zanwa, masoyi, Kuma Wakilin yaƙin neman takarar gwamnan Jihar Nasarawa na 2027 a J...

Daga Zubairu Lawal, Lafia

Wani matashin ɗan siyasa, Abbas Zanwa, masoyi, Kuma Wakilin yaƙin neman takarar gwamnan Jihar Nasarawa na 2027 a Jam'iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu Wadada, daga Gundumar Zanwa da ke Ƙaramar Hukumar Lafia ta Jihar Nasarawa, ya raba wa mata injinan niƙa guda 10, domin taimaka musu wajen samun sana’o’in dogaro da kai.

Abbas ya bayyana cewa, tallafin ya shafi mata ne, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke ƙarƙashin Gundumar Zanwa, inda ya ce burinsa shi ne ganin mata sun rungumi sana’o’in dogaro da kai domin rage musu raɗaɗin talauci.

Ya ce, “Burina shi ne ganin mata sun rungumi sana’o’in dogaro da kai. Ina da burin taimaka wa mata da matasa domin kowa ya samu abin yi.”

A cewarsa, a wannan karon ya raba injinan niƙa guda 10 ga mata, tare da bai wa wasu mata 100 tallafin kuɗi na Naira 10,000 kowacce.

Abbas ya ƙara da cewa, nan gaba zai duba wasu unguwanni domin gudanar da irin wannan tallafi, yana mai cewa irin waɗannan shirye-shirye za su taimaka wajen rbunkasa   tattalin arziki da rage radadin talauci a tsakanin al’umma.

“Abin da na yi, ko da siyasa ce, yana da kyau. Duk wanda yake neman ƙuri’a daga mutane, ya kamata ya yi musu abin da zai taimaka musu su dogara da kansu,” in ji shi.

Da yake magana kan siyasar Jihar Nasarawa, Abbas Zanwa ya bayyana cewa shi masoyin ɗan takarar gwamnan Jihar Nasarawa  2027 a Jam'iyyar APC Ahmad Aliyu Wadada, ne, kuma ya yi alkawarin kawo masa ƙuri’u masu yawa a lokacin zaɓe.

Ya ce yana da yakinin cewa, insha  Allah  Ahmad Aliyu Wadada zai zama Gwamnan Jihar Nasarawa, tare da yin alkawarin cewa gwamnatin sa za ta taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar.

Abbas ya ce ya amince da tsarin siyasar Wadada, musamman yadda ya ce ɗan siyasar ba ya cin mutuncin mutane, kuma yana girmama jama’a tare da sanin ya kamata.

Ya bayyana Wadada a matsayin mutum mai kishin ci gaban al’umma, yana mai cewa idan ya zama gwamna, zai samar da yanayi na walwala da kuma damar samun ayyukan yi ga matasa da sauran jama’a.

 taron da aka gudanar a Kasuwar Alhamis ranar Lahadi, maza da mata daga sassa daban-daban sun halarta, ciki har da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa, kamar Dan Takarar kujerar Majalisan Lafia ta tsakiya Barrister Abubakar Imam Zanwa da Babban mataimakin Gwamnan Nasarawa Muhammad Abubakar da sauran Masu riqe da madafun iko.

Haka kuma, an karɓi wasu waɗanda suka sauya sheƙa daga tafiyar tsohon Sifeto Janar na Ƙasa, Muhammad Adamu Abubakar, zuwa tafiyar Ahmad Aliyu Wadada Dan Takarar Jam'iyyar APC.

Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin mutane 145 ne suka sauya sheƙa zuwa goyon bayan Wadada daga Gundumar Zanwa da ke Ƙaramar Hukumar Lafia.

Jama’a da dama da suka halarci taron sun bayyana ra’ayoyinsu kan muhimmancin tallafawa mata da matasa, tare da jaddada buƙatar samar da sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwar al’umma.
 

No comments