Daga Bello Hamza, Abuja A siyasa, ba koyaushe ake cin zabe da ƙuri'u ba; sau da yawa ana fara cin nasara ne ta hanyar rinjayar tunanin a...
A siyasa, ba koyaushe ake cin zabe da ƙuri'u ba; sau da yawa ana fara cin nasara ne ta hanyar rinjayar tunanin al'umma. Duk wanda ya mallaki ajandar tattaunawa, shi ne ke da rinjaye a zuciyar masu sauraro. Wannan shi ne dalilin da ya sa waƙoƙin siyasa suka zama wani muhimmin makami a siyasar Nijeriya.
A yau, babu shakka Dauda Kahutu Rarara ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan siyasa da suka fi iya sauya alƙiblar tattaunawar jama'a. Waƙoƙinsa, ba wai don nishaɗi kawai ake sauraro ba; ana sauraronsu ne domin a gano saƙon siyasa da ke cikinsu. Shi ya sa duk lokacin da ya fitar da waƙa, musamman a lokacin da siyasa ke ɗaukar zafi, mutane kan tsaya su saurara.
Abin da ya faru a Gombe cikin 'yan kwanakin nan ya sake tabbatar da hakan.
Kodayake Rarara bai ambaci sunan kowa kai tsaye ba, masu bibiyar siyasar Gombe sun yi ta fassara waƙoƙinsa da cewa suna nuni ga tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. Ko wannan fassarar ta yi daidai ko a'a, ba shi ne babban abin dubawa ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa waƙoƙin sun sauya ajandar tattaunawar siyasar jihar.
Tun kafin fitowar waƙoƙin, ana tattauna makomar siyasa Pantami, kalamansa, danfane da yadda yake shagube da kuma ƙage ga ‘Yan adawa. Bayan fitowar waƙoƙin kuwa, tattaunawar ta sauya. An fara magana ne kan hotonsa na siyasa, yadda yake fuskantar suka da kuma tambayoyin da ake tasowa da su game da shi. Wannan shi ne babban tasirin waƙar siyasa.
A siyasa, ba koyaushe ake buƙatar tabbatar da zargi kafin ya yi tasiri ba. Abin da ke da muhimmanci shi ne ya zama babban abin tattaunawa. Idan ɗan takara ya shafe lokacinsa yana ƙoƙarin gamsarwa ko kare kansa maimakon gabatar da manufofinsa, to ya riga ya rasa wani bangare na filin fafatawa.
Abin da ya sa waƙoƙin Rarara suka fi ɗaukar hankali shi ne yadda suka tilasta wa magoya bayan Pantami fita kafafen sada zumunta domin kare shi. Wannan shi kaɗai alama ce cewa waƙoƙin sun taba wata jijiyar siyasa. Da ba su yi tasiri ba, da ba a ga irin wannan gaggawar mayar da martani ba.
Wani muhimmin darasi a siyasa shi ne, ba lallai ne wanda ya fara kare kansa ya kasance ya yi laifi ba. Amma idan ya kasa dawo da tattaunawar zuwa kan manufofinsa, abokan hamayyarsa sukan ci gaba da sarrafa ajandar siyasa. Wannan shi ne abin da ke fuskantar Pantami a halin yanzu.
Akwai kuma wani batu da ba za a iya kauce masa ba. Pantami ya fice daga APC yana mai sukar yadda aka gudanar da harkokin cikin gida na jam'iyyar, musamman batun adalci. Yanzu da yake neman jagoranci a wata jam'iyya, sai ya aikata irin abin da ya yi zargi na "rashin adalci", mutane za su yi masa tambayoyi iri ɗaya da ya riƙa yi wa wasu. Wannan ba zalunci ba ne; wannan shi ne siyasa.
A siyasa, jama'a ba sa son ganin ɗan siyasa yana amfani da ma'auni biyu. Idan ka gina sunanka kan gaskiya da adalci, za a sa ran ka kasance cikin shiri don amsa duk wata tambaya da ta shafi rayuwarka ta siyasa ko ta gwamnati. Wannan shi ne farashin jagoranci.
Haka kuma, fitowar sanarwar wata ƙungiyar ba ta gwamnati ba, NGO ta 'Concerned Gombe Citizens' a ranar 3 ga Agustan 2026, inda ta buƙaci hukumomin da abin ya shafa su binciki wasu zarge-zargen da ake yaɗawa ya ƙara dora batun a gaban jama'a.
Kodayake wannan ba yana nufin an tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba ne, kuma bincike ne kaɗai zai iya fayyace gaskiya, amma ta fuskar siyasa, irin waɗannan abubuwa kan ƙara tsawaita muhawara tare da sanya ɗan takara cikin yanayin kare martabarsa, kuma hakan na dusashe tasirinsa.
A nan ne tasirin waƙar Rarara ya fito fili. Waƙar ba ita ce ta haifar da waɗannan tambayoyi ba, amma ta taimaka wajen kambama su, da sa su zama babban abin tattaunawa. Wannan shi ne ainihin karfin sadarwar siyasa.
Wani mai sharhi daga Gombe, Tasiu Abubakar, ya bayyana cewa ana bai wa tasirin Pantami girma sosai a shafukan sada zumunta fiye da yadda yake a siyasar cikin gida. A cewarsa, yawancin masu yada sakonnin siyasar Pantami ba mazauna Gombe ba ne, kuma hakan na iya sa mutane su dauka cewa yana da farin jini fiye da yadda yake a zahiri a Jihar Gombe
A siyasar yau, ba wai abin da ka fada kadai ake saurara ba; abin da mutane suke fada a kanka ma yana da tasiri.
Masanin nazarin wakoki da al'adun siyasa, Muhammad Saddiku daga Kaduna, ya bayyana cewa babban ma'aunin tasirin waka shi ne irin martanin da take haifarwa. A cewarsa, da ace wakokin ba su da tasiri, da ba za su mamaye tattaunawar kafafen sada zumunta ba. Ya ce yadda magoya baya da masu adawa suka fito suna kare matsayinsu ko kuma suna goyon bayan abin da wakar ta kunsa ya nuna cewa wakar ta cimma manufarta ta jawo hankalin jama'a.
Wannan shi ya sa ake cewa yakin neman zave ba ya fara ranar da INEC ta ce a fara ba. Yana farawa ne daga ranar da al'umma suka fara magana a kanka. A wannan fage kuwa, Rarara ya nuna cewa har yanzu yana da ikon jawo hankalin jama'a da sauya alkiblar tattaunawa.
Ko hakan zai wadatar wajen raunana takarar Pantami? Muhammad Saddiku ya ce, tabbas hakan zai raunana siyasarsa domin a cewarsa siyasa cike take da abubuwan da ke sauyawa cikin gaggawa.
Watsi da tasirin irin wadannan wakoki, hakan kuskure ne. Tarihin siyasar Nijeriya ya nuna cewa wakokin siyasa sun kasance suna taimakawa wajen gina ko raunana hoton 'yan siyasa. Ba sa yanke zave su kadai, amma suna iya tasiri kan yadda masu zave ke kallon dan takara.
Saboda haka, abin da Rarara ya yi bai kamata a dauke shi a matsayin waka kawai ba. Dabara ce ta sadarwar siyasa wadda ta samu nasarar sauya abin da ake tattaunawa a Gombe. A maimakon mutane su rika magana kan abin da Pantami zai yi idan ya zama gwamna, an fi tattauna yadda yake fuskantar suka da tambayoyin da ake yi masa.
A siyasa, wannan ba karamin sauyi ba ne. Domin duk lokacin da dan takara ya daina jagorantar tattaunawa, ya koma bin tattaunawar da wasu suka kirkira masa, to ya shiga yanayin da zai yi ta mayar da martani maimakon gabatar da ajandarsa.
A ƙarshe, ko Pantami zai iya shawo kan wannan kalubale ko kuwa wakokin Rarara za su ci gaba da yin tasiri a kansa, lokaci ne zai bayyana. Amma abin da ya riga ya tabbata shi ne cewa Rarara ya sake nuna karfin wakar siyasa a matsayin makamin yakin tunani, domin a siyasa, wanda ya mallaki tunanin jama'a sau da yawa shi ne ke mallakar hanyar zuwa akwatin zave.
Bello, ya rubuto mana ne daga Abuja

No comments