Rundunar ’yan sandan Jihar Filato ta kama wani limamin coci da wasu jami’an tsaro biyu da ke kan aiki, bisa zargin cewa sun shirya sace mata...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato ta kama wani limamin coci da wasu jami’an tsaro biyu da ke kan aiki, bisa zargin cewa sun shirya sace matan wasu manyan bishop-bishop biyu a birnin Jos, babban birnin jihar.
An ce an kama mutanen ne bayan rundunar ’yan sandan ta samu sahihan bayanan sirri game da wata zargin makarkashiyar aikata laifi da kuma yunkurin sace matan da aka daƙile.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:10 na rana, ranar Juma’a, 7 ga Agusta, 2026.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana ɗaya daga cikin waɗanda aka kama da suna Rabaran Hassan Yunisim Mijah, mai shekaru 42, mazaunin Tudun Wada, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
A cewar bayanan da masani kan yaƙi da ta’addanci kuma manazarcin tsaro, Zagazola Makama, ya samu, ana zargin Mijah da haɗa baki da Sajan Ezra Sunday, jami’in Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, da kuma OS Usman Khalid, jami’in Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya, domin sace matan Bishop Ephraim Gongden da tsohon Bishop Benjamin Kwashi.
An ce jami’an sojan saman da na ruwan suna aiki ne a Sashe na 1 na Operation ENDURING PEACE (OPEP) da ke Jos, wata rundunar haɗin gwiwar hukumomin tsaro da aka kafa domin tabbatar da zaman lafiya da yaƙi da aikata laifuka a Jihar Filato.
Rahotannin sun ce bishop-bishop ɗin biyu mazauna yankin Rantya ne da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, inda ake zargin matan nasu suke da alaƙa da wuraren da waɗanda ake zargin suka shirya kai farmakin.
Bayan rundunar ’yan sanda ta samu bayanan sirri kan shirin, jami’anta suka fara wani samame cikin gaggawa domin dakile yunkurin sace matan.
An ce kwamandan Sashen Sa-kai da Amsa Laifuka (VCRU) ne ya jagoranci aikin, wanda ya kai ga cafke mutanen uku.
Bayan kama su, jami’an tsaro sun gudanar da bincike da yi musu tambayoyi, inda ake zargin waɗanda ake tuhumar sun amsa hannu a cikin shirin.
“Bayan yi musu tambayoyi, waɗanda ake zargin sun amsa aikata laifin,” inji rundunar ’yan sandan, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Rundunar ’yan sandan ta kuma sanar da shugabancin Operation ENDURING PEACE (OPEP) cewa an kama jami’an sojin saman da na ruwan da ke aiki a karkashin rundunar.
Lamarin ya jawo hankali musamman saboda zargin ya shafi jami’an Rundunar Sojin Sama da Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya da ke kan aiki, waɗanda ake zargin sun shiga cikin wani shiri na sace ’yan gidan manyan limaman Kirista.
Sai dai binciken jami’an tsaro na ci gaba da gudana domin gano cikakken bayani game da zargin makarkashiyar.
Hukumomin tsaro na kuma kokarin gano ko mutanen ukun sun shirya wannan shiri ne da kansu ko kuma suna aiki ne a matsayin wani ɓangare na babbar ƙungiyar masu aikata laifuka.
Haka kuma, ana ci gaba da ƙoƙarin gano tare da cafke wasu mutanen da ake zargin suna da hannu a cikin shirin.

No comments