Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan,...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce al’ummar Kano ba sa goyon bayan kalaman da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kan batun siyasar Musulmi da Musulmi a Nijeriya.
Kwankwaso ya bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya haifar da rarrabuwar kawuna da kuma kawo cikas ga haɗin kan al’umma.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan ya ce ya damu matuƙa da kalaman Sheikh Jingir da ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen makon da ya gabata.
Kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir, wanda ke cikin shugabannin ƙungiyar Izala, suka jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai.
Sheikh Jingir ya yi magana ne kan batun tikitin takarar shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi, lamarin da ya haifar da muhawara tsakanin jama’a.
Kwankwaso, wanda shi ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce abin damuwa ne yadda irin waɗannan kalamai ke fitowa daga bakin malamin da ke da matsayi da tasiri a cikin al’umma.
Ya ce bai kamata a yi amfani da matsayi ko murya wajen furta kalaman da za su iya kawo rarrabuwar kai tsakanin ’yan Nijeriya ba.
“Bai kamata mu yi amfani da muryarmu wajen faɗin kalaman da za su iya raunana haɗin kan ƙasarmu ba,” in ji shi.
Kwankwaso ya ƙara da cewa a halin da Nijeriya ke ciki yanzu, ya kamata shugabanni su guji duk wani furuci da zai iya haifar da rashin haɗin kai.
Ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya ya kamata ya zama abin da ya fi muhimmanci a wannan lokaci.
.jpg)
No comments