Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Tilasta Wasu Da Ake Zargi Su Tono Gawar Wanda Suka Kashe A Imo

Dakarun Birged na 34 na Sojojin Kakkabo, da ke gudanar da ayyuka ƙarƙashin Operation UDO KA, tare da ci gaba da Operation EASTERN SANITY II,...



Dakarun Birged na 34 na Sojojin Kakkabo, da ke gudanar da ayyuka ƙarƙashin Operation UDO KA, tare da ci gaba da Operation EASTERN SANITY II, sun gano wani kabari mara zurfi tare da fitar da gawar marigayi Cif Ibe Anyadu, shugaban al’ummar Aggah da ake zargin wasu ’yan ƙungiyar masu aikata laifuka ne suka kashe shi.

An gano gawar marigayin ne sakamakon wani samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri, wanda ya kai ga kama wasu da ake zargi da hannu a aikata manyan laifuka a yankin.

Binciken da jami’an tsaro suka yi bayan kama waɗanda ake zargin ya kai ga gano mutanen da ake zargi da kisan wani sojan Najeriya da kuma satar makaman aiki na sojoji. A yayin binciken, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya amsa cewa yana da hannu a kisan Cif Anyadu, tare da nuna wa sojojin inda aka binne gawarsa.


A ranar 2 ga Agusta, 2026, wanda ake zargin ya jagoranci dakarun zuwa wani kabari mara zurfi da ke cikin Dajin Umudike, wurin da ake zargin ƙungiyar masu aikata laifukan ke amfani da shi a matsayin sansani.

A nan ne sojojin suka tono gawar marigayin cikin nasara.

An gudanar da aikin tono gawar ne a gaban ’yan uwan marigayin, jami’an sa-kai daga Ƙaramar Hukumar Ohaji/Egbema, da kuma wakilan al’ummomin Aggah da Umudike.

Iyalin marigayin sun samar da akwatin gawa da motar ɗaukar gawa domin tabbatar da cewa an gudanar da jana’izar cikin mutunci, bisa al’adu da ɗabi’un al’ummar marigayin.

Sojoji sun yi alƙawarin ganin an yi wa marigayin adalci.

Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Kudu maso Gabas, Operation UDO KA, Manjo Janar Oluremi Ayobami Fadairo, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da addu’ar Allah Ya jiƙan sa, Ya kuma ba shi hutu na har abada.

Kwamandan ya kuma tabbatar wa iyalan Cif Anyadu da al’ummar Aggah cewa za a tabbatar da an yi musu adalci, yana mai cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa dokokin Tarayyar Najeriya.

Hedikwatar Operation UDO KA ta ce za ta ci gaba da ƙoƙarin wargaza ƙungiyoyin masu aikata laifuka a yankin Kudu maso Gabas, tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a aikata laifukan tashin hankali.

Rundunar ta kuma ce tana da niyyar tabbatar da cewa waɗanda laifukan suka shafa da iyalansu sun samu cikakken bayani da kwanciyar hankali ta hanyoyin da doka ta tanada.

Ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanan sirri masu inganci kuma cikin lokaci, domin hakan na da matuƙar muhimmanci wajen samun nasarar ayyukan da ake gudanarwa.

No comments