Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara rabon takin zamani kyauta ga kananan manoma 150,000 a fadin jihar, a wani mataki da ta ce zai taimaka wajen k...
An gudanar da rabon takin ne ta cibiyoyin karbar taki guda 69 da aka kafa a fadin kananan hukumomi 23 na jihar, inda kowace karamar hukuma ke da cibiyoyi uku.
Da yake duba yadda ake rabon takin a Cibiyar Karbar Taki ta Gadan Gayan da ke Karamar Hukumar Igabi, Kwamishinan Aikin Gona na jihar, Malam Murtala Dabo, ya ce an riga an kai takin zuwa rumbunan ajiya daban-daban a fadin jihar.
Ya ce an kuma tura jami’an tsaro da na fasahar sadarwa domin tabbatar da cewa rabon takin ya kasance cikin gaskiya, adalci da sahihanci.
A cewarsa, kowane manomin da aka tantance zai samu buhunan taki guda biyu ta hanyar amfani da tsarin zamani na tantance masu cin gajiyar shirin.
“Za a tura wa kowane wanda aka tantance sako da zai sanar da shi inda zai karbi buhunan taki guda biyu da Gwamna ya samar domin daminar shekarar 2026.
“Za a tantance takardar karbarsa, sannan a dauki bayanansa da hotonsa kafin a mika masa takin,” in ji shi.
Kwamishinan ya gargadi wadanda suka amfana da shirin da su yi amfani da takin kai tsaye a gonakinsu, yana mai jan kunnen duk wanda zai yi yunkurin karkatar da shi ko sayar da shi.
Ya ce takin ba na sayarwa ba ne, kuma duk wanda aka kama yana sayar da shi zai fuskanci hukunci.
“Wannan taki ba na sayarwa ba ne. Duk wanda aka samu yana sayar da shi za a kama shi kuma a gurfanar da shi gaban kotu. An samar da wannan tallafi ne musamman domin kananan manoma,” in ji Dabo.
Shi ma Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa rabon takin na daga cikin matakan da Gwamna Uba Sani ke dauka wajen kara zuba jari a bangaren aikin gona.
Ya ce kasafin kudin aikin gona na jihar ya karu daga kusan naira biliyan 1.4, wanda bai kai kashi daya cikin dari na kasafin jihar ba, zuwa sama da naira biliyan 100 a kasafin shekarar 2026, wanda ya kai kashi 11.6 cikin dari.
Maiyaki ya ce baya ga taki, gwamnatin jihar ta kuma tallafa wa manoma da taraktoci, rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da kuma injinan famfo, domin bunkasa noman damina da na rani
Daya daga cikin manoman da suka amfana da shirin daga Dandami, Unguwar Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Igabi, AbdulHamid Muhammad, ya yabawa gwamnatin jihar bisa tallafin.
“Na shuka masara kuma ina bukatar taki. Ya zo a daidai lokacin da nake bukatarsa. Ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma Gwamna Uba Sani bisa wannan tallafi,” in ji shi.
Shi ma Shugaban Karamar Hukumar Igabi, Sani Abdul, ya yabawa shirin, yana mai cewa kusan kashi 80 cikin dari na al’ummar karamar hukumar sun dogara ne da aikin gona domin samun abin dogaro da kai.
Ya ce tallafin zai taimaka wajen rage wa manoma radadin tsadar kayan aikin gona tare da kara samar da abinci a jihar.


No comments