Matattarar Labarai ta tattaro jerin laifukan hanya 51 da Dokar Hukumar Kula da Bin Dokokin Hanya ta Jihar Kaduna (KASTLEA) ta tanada, tare d...
Matattarar Labarai ta tattaro jerin laifukan hanya 51 da Dokar Hukumar Kula da Bin Dokokin Hanya ta Jihar Kaduna (KASTLEA) ta tanada, tare da adadin tarar da doka ta ƙayyade ga kowane laifi da sauran matakan hukunci da ka iya biyo baya.
Wannan bayani ya zama mai muhimmanci ga direbobi da sauran masu amfani da hanyoyi a Kaduna, musamman a lokacin da ake samun ƙorafe-ƙorafe daga wasu masu ababen hawa kan yadda wasu jami’an kula da zirga-zirga ke gudanar da aikinsu, ciki har da zargin neman kuɗaɗen da ba su cikin tarar da doka ta tanada, cin zarafi ko kuma karɓar kuɗi ba tare da bayar da cikakken bayani kan laifin da aka aikata ba.
Saboda haka, sanin ainihin tarar da KASTLEA ta tanada zai taimaka wa direba ya bambance tsakanin abin da doka ta ƙayyade da kuma wani kuɗi da ba ya cikin jadawalin hukuma. Haka kuma, wasu laifuka ba su tsaya kan biyan tara kawai ba; doka ta tanadi ƙarin matakai kamar ƙwace abin hawa, wato impoundment, kai wanda ya aikata laifin gaban kotu, wato prosecution, gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa, wato psychiatric test, gyaran abin hawa ko sauke abin da ya wuce kima, gwargwadon laifin.
Ga jerin laifukan da tararsu da sauran hukuncinsu:
Sharuɗɗan Lasisin Tuƙi (Gaba ɗaya):
1. Tuƙi ba tare da lasisin direba ba (Driving without a Driver’s Licence)
Lambar laifi: LGC-01
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A kulle ko ƙwace abin hawan na ɗan lokaci (impound vehicle).
2. Barin wanda bai kai shekara 18 ya tuƙa abin hawa (Driving of any vehicle by person under 18)
Lambar laifi: LGC-02
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa (impound vehicle).
3. Mai koyon tuƙi ba tare da izinin koyon tuƙi ba (Learner driving without Learner’s Permit)
Lambar laifi: LGC-03
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A sauke direban daga abin hawa (dislodge driver).
4. Mai koyon tuƙi a babbar hanya (major highway) ba tare da izini ba (Learner driving on major highway)
Lambar laifi: LGC-04
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A sauke direban daga abin hawa.
5. Mai koyon tuƙi ba tare da ƙwararren direba mai lasisi yana tare da shi ba (Learner driving unaccompanied by a licensed driver)
Lambar laifi: LGC-05
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
6. Tuƙin abin hawa mara lasisi (Driving an unlicensed vehicle)
Lambar laifi: LGC-06
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
7. Tuƙi da jabun lambar mota (Driving with fake number plates)
Lambar laifi: LGC-07
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa kuma a gurfanar da direban a gaban kotu.
8. Tuƙin mota mai lambar da ba ta ƙoƙe ko mai matsala (Driving a vehicle with unauthorised or defective reflective number plates)
Lambar laifi: LGC-08
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
9. Hawan babur ko keke mai ƙafa uku ba tare da lasisi ba (Riding an unlicensed motorcycle/tricycle)
Lambar laifi: LGC-09
Tara: ₦3,000
Ƙarin hukunci: A kulle babur ko keken mai ƙafafu uku.
Sharuɗɗan Lasisin Motocin Haya:
10. Rashin fentin motar haya da launukan da aka amince da su (Not painting a commercial vehicle in approved colours)
Lambar laifi: LCC-01
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A tilasta wa mai motar ya yi mata fenti yadda ya kamata.
11. Keta ƙa’idar hanyar da aka tanada wa motocin haya (Violation of route by commercial vehicles)
Lambar laifi: LCC-02
Tara: ₦5,000.
12. Rashin rubuta hanya da lambar mota a jikin abin hawa (Non-display of route and number on vehicle)
Lambar laifi: LCC-03
Tara: ₦3,000.
Alamomin Hanya da Layukan Zirga-Zirga:
13. Rashin bin alamomin hanya (Disobeying traffic signs)
Lambar laifi: TSM-01
Tara: ₦5,000.
14. Rashin bin fitilar zirga-zirga (Disobeying traffic lights)
Lambar laifi: TSM-02
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: Gwajin lafiyar kwakwalwa (psychiatric test).
15. Yin fakin a kan layin rawaya a kowace babbar hanyar jama’a (Parking on yellow line on any public highway)
Lambar laifi: TSM-03
Tara: ₦5,000.
16. Ƙetare layin rawaya biyu (Vehicle crossing double yellow line)
Lambar laifi: TSM-04
Tara: ₦10,000.
17. Yin fakin ba bisa ƙa’ida ba (Wrong parking)
Lambar laifi: TSM-05
Tara: ₦10,000.
18. Tsayawa a cikin akwatin mahadar da aka yi wa layin rawaya alama (Staying within the yellow junction box – off-side rule)
Lambar laifi: TSM-02
Tara: ₦5,000.
19. Rashin ba mai tafiya a ƙafa damar wucewa a mashigar Zebra (Failure to yield right of way to pedestrians at a Zebra Crossing)
Lambar laifi: TSM-06
Tara: ₦10,000.
20. Rashin ba motocin da ke gefen hagu damar wucewa a zagayen hanya (Failure to give way to traffic on the left at a roundabout)
Lambar laifi: TSM-07
Tara: ₦5,000.
Matsalar Abin Hawa (Vehicle Defect):
21. Tuƙin babur ko keke mai ƙafa uku da fitilunsa ba sa aiki (Driving motorcycles/3-wheelers with non-functional lamps)
Lambar laifi: VDF-01
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A gyara fitilun.
22. Tuƙin motar haya ko ta ƙashin kai mai fitilun da ba sa aiki (Driving private motor vehicles with non-functional lamps)
Lambar laifi: VDF-02
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A gyara matsalar.
23. Tuƙin motar haya da fitilun da ba sa aiki (Driving commercial vehicles with non-functional lamps)
Lambar laifi: VDF-03
Tara: ₦25,000
Ƙarin hukunci: A gyara matsalar.
24. Tuƙin tirela ko motar ɗaukar kaya mai tirela da fitilun da ba sa aiki (Driving trailers, tankers and tippers with non-functional lamps)
Lambar laifi: VDF-04
Tara: ₦100,000
Ƙarin hukunci: A gyara matsalar.
Barasa da Miyagun Ƙwayoyi:
25. Tuƙi a ƙarƙashin tasirin barasa ko ƙwayoyi (Driving under the influence of alcohol and/or drugs)
Lambar laifi: ALD-01
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
26. Shan sigari yayin tuƙi (Smoking while driving)
Lambar laifi: ALD-02
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa kuma a yi wa direban gwajin lafiyar kwakwalwa.
Laifukan Masu Hawan Babura:
27. Hawan babur ba tare da hular kariya ba (Riding of motorcycle without crash helmet for rider)
Lambar laifi: MCL-01
Tara: ₦2,000
Ƙarin hukunci: A kulle babur.
28. Hawan babur ba tare da izinin mai koyon tuƙi ba (Riding a motorcycle without a Learner’s Permit)
Lambar laifi: MCL-02
Tara: ₦2,000
Ƙarin hukunci: A kulle babur.
29. Hawan babur a sabanin hanyar zirga-zirga ta tsakiyar hanya (Riding a motorcycle against traffic through road median)
Lambar laifi: MCL-03
Tara: ₦3,000
Ƙarin hukunci: A kulle babur.
30. Ɗaukar fasinjoji fiye da yadda aka yarda a babur (Conveying more than one passenger at any given time)
Lambar laifi: MCL-04
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A kulle babur, sannan fasinjan ya biya ₦500.
31. Sanya na’urar kiɗa a babur (Installation of musical gadgets on a motorcycle)
Lambar laifi: MCL-04
Tara: ₦3,000
Ƙarin hukunci: A ƙwace na’urar kiɗan.
32. Sauya tsarin babur daga yadda masana’anta ta ƙera shi (Alteration of manufacturer’s specification on motorcycle)
Lambar laifi: MCL-05
Tara: ₦3,000.
33. Tsayayya da kame da jami’an tsaro ko zirga-zirga (Motorcycle/Tricycle resisting arrest)
Lambar laifi: MCL-06
Tara: ₦3,000.
Laifukan Wuce Iyakar Gudu:
34. Wuce iyakar gudun da aka ƙayyade (Exceeding prescribed speed limit)
Lambar laifi: SPV-01
Tara: ₦5,000.
35. Bin motar gaggawa a bayanta (Tailing an emergency vehicle)
Lambar laifi: SPV-01
Tara: ₦10,000.
36. Rashin matsar da abin hawa mai tafiya a hankali zuwa layin dama (Failure of slow-moving vehicle to keep to the right lane)
Lambar laifi: SPV-02
Tara: ₦5,000.
Sauran Laifukan Zirga-Zirga:
37. Kai hari ga jami’in zirga-zirga (Assault on a Traffic Officer)
Lambar laifi: MTF-01
Tara: ₦50,000
Ƙarin hukunci: A ƙwace abin hawa kuma a gurfanar da wanda ya aikata laifin a kotu.
38. Tuƙi a hanyar da dokar zirga-zirga ta haramta (Driving in a direction prohibited by the Road Traffic Law)
Lambar laifi: MTF-02
Tara: ₦25,000
Ƙarin hukunci: Gwajin lafiyar kwakwalwa da gurfanarwa a kotu.
39. Juya mota ba bisa ƙa’ida ba (Illegal U-turns)
Lambar laifi: MTF-03
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
40. Wuce wata mota ba bisa ƙa’ida ba (Wrong overtaking of other vehicles)
Lambar laifi: MTF-04
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
41. Lodawa motar haya kaya ko fasinjoji fiye da kima (Overloading of a commercial vehicle)
Lambar laifi: MTF-05
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: A sauke abin da ya wuce ƙima kuma a kulle abin hawa.
42. Tsayawa ko ɗaukar fasinjoji a wajen da ba tashar mota ba (Parking or stopping to pick passengers by a commercial vehicle other than at designated bus stop)
Lambar laifi: MTF-06
Tara: ₦20,000
Ƙarin hukunci: Horar da direba (driver training) da kuma kulle abin hawa.
43. Tuƙin abin hawa a hanyar da dokar zirga-zirga ta haramta (Driving vehicle in a direction prohibited by the Road Traffic Law)
Lambar laifi: MTF-07
Tara: ₦300,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa kuma a gurfanar da direban a kotu.
44. Barin mota a kan babbar hanya cikin dare (Abandoned vehicle on highway overnight)
Lambar laifi: MTF-08
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
45. Hana zirga-zirga a babbar hanya (Causing obstruction on highway)
Lambar laifi: MTF-09
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A kulle abin hawa.
46. Fasinja yana rataye a bayan abin hawa yayin tafiya (Commuter hanging on tailboard of moving vehicle)
Lambar laifi: MTF-10
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: A sauke fasinjan.
47. Tuƙi da ƙofofin mota a buɗe (Driving vehicles with doors left open)
Lambar laifi: MTF-11
Tara: ₦5,000.
48. Yin ko karɓar kiran waya yayin tuƙi (Making or receiving phone calls while driving)
Lambar laifi: MTF-12
Tara: ₦10,000
Ƙarin hukunci: A gurfanar da direban a kotu.
49. Tuƙi ba tare da ɗaure bel ɗin kujera ba ga direba da fasinjan gaba (Driving without a strapped seat belt for both driver and front seat passengers)
Lambar laifi: MTF-13
Tara: ₦2,000
Ƙarin hukunci: ₦1,000 domin ɗaure/gyara bel ɗin kujera.
50. Rashin sanya alamar gargadin abin hawa mai matsala (Failure to display reflective warning triangle sign at point of breakdown)
Lambar laifi: MTF-14
Tara: ₦5,000
Ƙarin hukunci: ₦2,000.
51. Mai mota ko direba ya ƙi bin umarnin kame (Motorist resisting arrest)
Lambar laifi: MTF-15
Tara: ₦5,000.

No comments