Daga Zubairu Muhammed Lawal Tatita, Lafia Dan Takarar Gwamnan Jihar Nasarawa karkashin Jam'iyyar SDP Tsohon Sifeto Janar na ’Yan Sandan ...
Daga Zubairu Muhammed Lawal Tatita, Lafia
Dan Takarar Gwamnan Jihar Nasarawa karkashin Jam'iyyar SDP Tsohon Sifeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar (Walin Lafia), ya tallafa wa manoma a yankin Nasarawa ta Yamma da kayan aikin gona da kuɗinsu ya kai miliyoyin naira.
Da yake jawabi yayin rabon tallafin, Mohammed Adamu Abubakar ya shawarci manoman da suka amfana da su yi amfani da kayan aikin yadda ya kamata, tare da guje wa sayar da su.
Ya ce bai kamata a bai wa mutum kayan da zai amfana da su tsawon shekaru, sannan ya sayar da su domin biyan bukatun kwana ɗaya ko shekara ɗaya ba.
A cewarsa, an zaƙulo manoman da suka amfana ne daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomin yankin domin su samu damar cin gajiyar tallafin.
“Mun duba buƙatar al’umma, musamman yadda za a samu abinci mai yawa a Jihar Nasarawa. Kuma dole ne a yi amfani da kayan aikin gona na zamani.
Duk da cewa suna da tsada, idan muka taimaka muku da su, za ku samar da abinci mai yawa ga al’umma,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa babban abin da manomi ke bukata shi ne kayan aikin da zai taimaka masa wajen bunƙasa noma da ƙara yawan amfanin gona.
Kayan aikin da aka rabawa manoman Tallafin ya ƙunshi ƙananan taraktocin hannu guda 200, buhunan takin zamani guda 2,500, magungunan gona guda 1,800, injinan ban ruwa guda 60, gorar feshi guda 100, kekunan ɗaukar kaya guda 100, wulbaro guda 100, da kuma fatanya da shebur.
Haka kuma, an ware tallafin kuɗi ga kowace daga cikin gundumomi 59, wanda jimillarsa ta kai miliyan Naira 59.
Tallafin ya shafi al’ummomin yankin Nasarawa ta Yamma, waɗanda suka haɗa da ƙananan hukumomin Karu, Keffi, Kokona, Nasarawa da Toto, daga gundumomi 59.
A nasa jawabin, Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Mohammed Adamu Abubakar a Jam’iyyar SDP, Alhaji Abdullahi Yammani, ya jaddada wa magoya bayansa cewa Mohammed Adamu Abubakar yana nan daram wajen shirin tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a ƙarƙashin Jam’iyyar SDP a zaɓen 2027.
Yammani ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su ƙara himma wajen ganin an samu sauyin gwamnati a jihar.
Ya ce al’ummar Jihar Nasarawa sun gaji da abin da ya kira “mulkin mallaka” na Jam’iyyar APC, yana mai cewa SDP za ta kawo sauyin gwamnati da zai taimaka wa al’ummar jihar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su fito kwai da kwarkwata domin kada kuri’unsu, tare da tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri’un a gabansu kuma an bi tsarin kare ƙuri’a har zuwa inda ya dace.
A nata jawabin, Hajiya Khadija ta bayyana farin cikinta da tallafin, tana mai cewa irin wannan tallafi abu ne da ba a saba ganin irinsa ba a Jihar Nasarawa, musamman ganin cewa manoma sun samu kayan aikin gona masu yawa daga wani mutum ba tare da kasancewar tallafin gwamnati ba.
Ta tuno cewa a baya, matar tsohon Sifeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Hajiya Rukayya Abubakar, ta rika ziyartar kauyuka tare da rabawa mata tallafi domin inganta rayuwarsu.
Ta ce yanzu ma Mohammed Adamu Abubakar ya ci gaba da wannan kyakkyawan aiki da kansa, ta hanyar tallafawa manoma da kayan aikin gona domin su samu damar inganta noma da rayuwarsu.

No comments