Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ɗan Siyasar Da Ya Rantse Da Alƙur’ani Zai Yi Biyayya Ga Kwankwaso, Ya Koma APC

Kabiru Adamu Abdullahi, wani ɗan siyasa kuma tsohon aminin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga Jam’iyyar NDC, i...




Kabiru Adamu Abdullahi, wani ɗan siyasa kuma tsohon aminin jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga Jam’iyyar NDC, inda ya koma Jam’iyyar APC.

Abdullahi, wanda a baya ya rantse da Alƙur’ani domin tabbatar da amincinsa ga Kwankwaso bayan rabuwarsa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga NDC cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban jam’iyyar na Unguwar Kofar Ruwa, da ke ƙaramar hukumar Dala a Kano.

A cikin wasiƙar, Abdullahi ya ce rashin gamsuwa da abin da ya bayyana a matsayin “alkawuran da ba a cika ba” a cikin NDC ne ya sa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa daga yanzu zai mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zaɓensa a ƙarƙashin tutar APC.

Abdullahi ya ce: “Na shafe shekara 29 tare da Kwankwaso, amma abin da na samu shi ne alƙawuran da ba a cika ba. Zan koma inda za a fi girmama ni.”

A wasiƙar murabus ɗin tasa, ya gode wa NDC bisa damar da ta ba shi na yin hidima a jam’iyyar, amma ya bayyana cewa ya janye cikakken goyon bayansa daga jam’iyyar, inda murabus ɗin ya fara aiki nan take.

No comments