Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta bari matatun man fetur na Nalijeriya su lalace ba, yana mai cewa za a sake ...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta bari matatun man fetur na Nalijeriya su lalace ba, yana mai cewa za a sake fasalin yadda ake tafiyar da su ta hanyar bincike mai zurfi, sake fasalin tsarin gudanarwa da samar da ingantaccen shugabanci domin su koma aiki tare da samar da riba.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG), ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Salimon Akanni Oladiti.
Shugaban Ƙasar ya ce matsalolin da ke addabar matatun za a magance su ne ta hanyar tsari mai inganci da ya dogara da hujjoji, maimakon ɗaukar matakan wucin gadi. Ya ce za a gudanar da cikakken bincike da tantancewar ƙwararru domin gano matsalolin tsarin gine-gine, aiki, kuɗi da gudanarwa da ke hana matatun samar da abin da aka gina su domin yi. Ya jaddada cewa ganin wuta da hayaƙi daga matatar mai ba shi ne ma’aunin nasara ba, sai matatar ta samar da ƙima tare da riba.
Tinubu ya kuma ce Gwamnatin Tarayya na duba batutuwan da suka shafi aiwatar da ‘yancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, musamman batutuwan kundin tsarin mulki da ke da alaƙa da lamarin. Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su fahimci matakan da ake ɗauka. Haka kuma, ya tuna da tsohon shugaban NUPENG, marigayi Frank Kokori, yana mai cewa sun yi gwagwarmayar kafa tsarin dimokuraɗiyya tare.
Shugaban Ƙasar ya kuma yi alkawarin ƙara bai wa NUPENG damar shiga cikin aiwatar da shirin Shugaban Ƙasa na amfani da CNG, tare da ƙalubalantar ƙungiyar da ta tabbatar da cewa amfanin shirin ya isa ga masu sufuri.
A nasa jawabin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya yaba wa NUPENG bisa amincewa da sakamakon wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa. Ya ce irin wannan fahimta ta taimaka wajen rage saɓani tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da gwamnati. Idris ya ambaci cire tallafin man fetur da kuma ayyukan gina ababen more rayuwa a faɗin ƙasar a matsayin manyan sauye-sauyen da ƙungiyar ta yaba da su.
Shugaban NUPENG, Salimon Oladiti, ya yaba wa Tinubu kan cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya taimaka wajen dakile asarar dimbin kuɗaɗen gwamnati da kuma buɗe damar zuba jari a ababen more rayuwa. Ya kuma yaba da ayyukan manyan tituna, musamman hanyar Lagos–Calabar mai tsawon kilomita 750 da kuma babbar hanyar Sokoto–Badagry mai tsawon kilomita 1,068. Daga bisani, shugabannin NUPENG suka naɗa Tinubu a matsayin Babban Uban ƙungiyar.


No comments