A Nijeriya, tsayar da mutum a hanya da jami’an ’yan sanda ba sabon abu ba ne. Wani lokaci bincike ne na yau da kullum, wani lokaci kuma jami...
A Nijeriya, tsayar da mutum a hanya da jami’an ’yan sanda ba sabon abu ba ne. Wani lokaci bincike ne na yau da kullum, wani lokaci kuma jami’an tsaro na neman bayanan da za su taimaka wajen daƙile laifi. Amma abin da ya kamata ya zama bincike na tsaro na iya rikiɗewa zuwa tashin hankali, cin zarafi ko wuce gona da iri a wasu lokuta.
Akwai masu amfani da damar da suke da ita wajen muzanta direbobi, yi musu barazana ko tilasta musu bin umarnin da bai dace ba. Wasu kuma kan buƙaci a duba wayar salula ta mutum ko bincika bayanansa ba tare da bayyana dalilin da ya sa suke yin hakan ba—alhali an taɓa bayar da umarnin da ya hana jami’an ’yan sanda yin binciken wayoyin mutane ba bisa ƙa’ida ba.
To, idan aka tsayar da kai a hanya, me ya kamata ka yi? Mene ne haƙƙinka? Me ya kamata ka guje wa aikatawa? Kuma a wane lokaci ne tsayar da mutum ko binciken kayansa ya zama cin zarafi ko wuce gona da iri?
A cikin wannan rahoto, Matattarar Labarai ta binciki waɗannan tambayoyi domin taimaka wa direbobi da sauran masu amfani da hanya su san yadda za su kare kansu, su mutunta jami’an tsaro, sannan su guji shiga matsala yayin da suke mu’amala da ’yan sanda.
1. Kada Ka Firgita Ko Ka Fara Gardama:
Abu na farko shi ne ka natsu. Tsayawa da ’yan sanda ba yana nufin kai mai laifi ba ne. Ka rage gudu, ka tsaya lafiya, sannan ka yi magana cikin ladabi.
Haka kuma, kada ka yi yunƙurin guduwa ko yin abin da zai sa jami’in ya ɗauka kana ƙoƙarin guje wa bincike.
2. Tambayi Dalilin Tsayar Da Kai Cikin Ladabi:
Idan jami’in ya tsayar da kai, kana iya tambayar sa cikin mutunci dalilin da ya sa aka tsayar da kai. Rundunar ’yan sandan Nijeriya ma ta bayyana cewa mutum yana da damar neman sanin dalilin kama shi, kuma yana iya neman jami’in ya bayyana kansa idan bai bayyana ba.
Misali:
“Ranka daɗe, don Allah, me ya sa kuka tsayar da ni?”
Wannan ya fi a kan zagi, gardama ko ɗaga murya.
3. Idan Aka Nemi Binciken Motarka, Ka Ba Da Haɗin Kai Cikin Doka:
Dokar ’Yan Sandan Nijeriya ta 2020 ta tanadi ikon jami’in ’yan sanda na tsayarwa da bincika a wasu yanayi.
Amma bai kamata mutum ya ɗauki wannan a matsayin izinin yin komai ba. Dokar ta kuma tanadi matakan da ya kamata a bi kafin da lokacin bincike.
Saboda haka, idan jami’in ya ce zai binciki motarka, kada ka yi turjiya ko ƙoƙarin hana shi da ƙarfi. Idan kana ganin akwai abin da bai dace ba, ka lura da abin da ke faruwa, ka rubuta bayanan jami’in da wuri da yanayi idan hakan zai yiwu cikin aminci, sannan ka bi hanyar ƙorafi daga baya.
4. Kada Ka Sanya Kanka Cikin Haɗari Saboda Waya:
Mutane da yawa suna iya son ɗaukar bidiyo yayin da ake bincikarsu. Amma idan yanayin ya yi zafi, kada ka mayar da wayar abin da zai jefa ka cikin haɗari.
Muhimmin abu shi ne tsaronka da farko. Za ka iya tattara bayanan abin da ya faru daga baya.
5. Idan Aka Kama Ka, Ka San Haƙƙinka:
Idan lamarin ya koma daga tsayawa zuwa kame, yanayin ya canja.
Rundunar ’yan sandan Nujeriya ta bayyana cewa wanda aka kama yana da damar tambayar dalilin kamarsa, kuma yana iya neman sanar da ɗan uwansa, amintaccen mutum ko lauya.
Haka kuma, tanade-tanaden Dokar ’Yan Sanda ta 2020 sun ƙarfafa haƙƙin wanda ake zargi wajen sanin dalilin kama shi, samun damar tuntubar lauya da kuma sanar da na kusa da shi.
6. Kada Ka Rattaba Hannu Kan Abin Da Ba Ka Fahimta Ba:
Idan aka nemi ka rubuta bayani, kar ka yi gaggawar sanya hannu a kan takardar da ba ka karanta ko fahimta ba.
Rundunar ’yan sanda ta kuma bayyana cewa mutum na iya ƙin rubuta ko sanya hannu kan bayani, musamman idan yana ganin hakan na iya jefa shi cikin matsala; neman shawarar lauya na iya zama muhimmiyar hanya a irin wannan yanayi.
7. Idan Ka Ga An Tauye Maka Haƙƙi, Kada Ka Rama Da Ƙarfi:
Idan ka yi zargin cewa jami’in ya wulakanta ka, ya karɓi kuɗi ba bisa ka’ida ba, ya yi amfani da ƙarfi fiye da kima ko ya tauye wani haƙƙinka, kar ka rama da faɗa ko kai masa hari.
Ka tattara bayanan da za su taimaka wajen ƙorafi: sunan ko lambar jami’in idan kana da ita, wurin da abin ya faru, lokaci, motar sintiri ko ofishin da jami’an suke, da kuma sunayen shaidu idan akwai.
Rundunar ’yan sandan Nijeriya tana da Sashen Karɓar Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a (Police Complaint Response Unit — CRU) domin karɓar ƙorafe-ƙorafe kan jami’anta.
Abu mafi muhimmanci
Sanin haƙƙinka ba yana nufin ka yi wa jami’in ’yan sanda rashin kunya ba. Haka kuma, kasancewarka ɗan ƙasa ba yana nufin jami’i yana da damar tauye maka haƙƙi ba.
A hanya, abin da ya fi muhimmanci shi ne ka natsu, ka yi magana cikin ladabi, ka bi umarnin da ya dace da doka, sannan ka kare haƙƙinka ta hanyar da ba za ta jefa ka cikin haɗari ba.
Wannan shi ne bambanci tsakanin sanin haƙƙi da neman rikici.

No comments