Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Kotun Laifukan Talla Domin Ƙarfafa Tsarin Gudanar Da Harkar Talla

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar Kotun Laifukan Talla, a wani mataki na ƙarfafa tsari da sa ido kan harkar talla, inganta ƙwarewa da...

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar Kotun Laifukan Talla, a wani mataki na ƙarfafa tsari da sa ido kan harkar talla, inganta ƙwarewa da tabbatar da bin ƙa'ida a masana'antar talla da sadarwar kasuwanci a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wurin ƙaddamar da kotun a Abuja, yana mai bayyana kafa kotun a matsayin wani muhimmin mataki wajen gina masana'antar talla mai ƙwarewa da ɗaukar nauyi.

Ya ce: “Mu gina masana'antar talla da za ta yi fice wajen ƙirƙire-ƙirƙire, ta samu amincewar jama'a kuma ta kiyaye ɗaukar nauyi."

Ministan ya ce Dokar Majalisar Kula da Harkokin Talla ta Nijeriya (ARCON) mai lamba 23 ta shekarar 2022 ta faɗaɗa ikon hukumar na tsarawa da sa ido kan harkar talla, tare da tanadar da kafa kotun domin sauraron laifukan da suka shafi dokar da kuma ƙa'idoji da dokokin da suka shafi harkar talla.

Ya buƙaci sabuwar kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Cecilia M. A. Olatoregun, da ta gudanar da ayyukant ta cikin gaskiya, 'yanci da adalci.

A cewar sa, “Duk wata shari'a da aka gabatar a gaban ku, ku duba ta bisa hujjojin da ke cikin ta, ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, ko ƙauna ko ƙiyayya. Dole kotun ta kasance, kuma a gan ta a matsayin hukuma mai adalci da rashin nuna son kai." 

Idris ya taya shugabar da sauran membobin kotun murna, tare da tabbatar masu da ci gaba da goyon bayan ma'aikatar ga ARCON da ƙoƙarin gina masana'antar talla da za ta iya yin gogayya a duniya.

Tun da farko, Darakta-Janar na ARCON, Dakta Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, ya bayyana ƙaddamar da kotun a matsayin wani babban mataki wajen ƙarfafa tsari da bin ƙa'idoji a masana'antar talla.

“Kotun Laifukan Talla wata babbar dama ce ga masana'antar talla ta Nijeriya. Ita ce irin ta ta farko a duniya, domin Nijeriya ta ɗauki matakin hangen nesa, ba wai kawai wajen kafa dokoki kan harkar talla ba, har ma da samar da tsare-tsare da tsarin gudanarwa,” inji Fadolapo.

Shugabar Kotun Laifukan Talla, Mai Shari'a Cecilia M. A. Olatoregun, ta yi alƙawarin cewa sabuwar kotun za ta gudanar da ayyukan ta cikin gaskiya, adalci da ƙwarewa.

“Babban abin alfahari ne a kira mu domin yi wa ƙasar mu hidima, kuma mun ɗauki wannan nauyi da muhimmanci sosai. An buƙace mu da yin aiki cikin gaskiya, kuma wannan shi ne abin da za mu yi,” inji ta.

Membobin kotun sun haɗa da Musa Ahmed Attah, SAN; Merga Tyowanan Kachina, Esq.; Dakta Ken Onyeali Ikpe, FRPA; da Hajiya Sa’a Ibrahim, RPA.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babbar Sakatare ta Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire; Darakta mai kula da Sadarwar Jama'a da Wayar da Kai na Ƙasa, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama'a da Ƙa'idojin Gudanarwa, Dakta Suleiman Haruna; da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Gudanarwa ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Sunday Baba, da sauran manyan baƙi.



 

No comments