Daga Zubairu Lawal, Lafia Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi gargaɗi ga masu ƙoƙarin amfani da harkokin siyasa wajen tayar da fitina, tare da ba...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi gargaɗi ga masu ƙoƙarin amfani da harkokin siyasa wajen tayar da fitina, tare da bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar ba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa, Shuaibu Magaji Labaran, Ph.D., SAN, ya sanya wa hannu a ranar 10 ga Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce gwamnati ta lura cikin damuwa da wasu abubuwan da ke faruwa a yayin harkokin siyasa a jihar, wadanda suka hada da cin zarafi, toshe hanyoyin zirga-zirga ba bisa ƙa’ida ba, lalata tutoci da allunan tallan siyasa, tunzura jama’a, da kuma kai hare-hare kan wasu ’yan kasa masu bin doka, duk da sunan siyasa.
Gwamnatin ta ce irin wadannan ayyuka na iya haifar da barazana ga tsaro, zaman lafiya da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’ummar jihar.
Ta kuma jaddada cewa ba ta hana kowane mutum goyon bayan dan takarar da yake so a kowace jam’iyyar siyasa ba a babban zaben shekarar 2027, matuƙar ana yin hakan cikin iyakokin doka.
Sai dai gwamnatin ta yi gargaɗin cewa ba za ta amince da duk wani yunƙuri ko aiki da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar ba.
A cewar sanarwar, yunƙurin da wasu mutane ke yi na hura wutar siyasa da tayar da zafin siyasa abin Allah-wadai ne, saboda hakan na iya yin illa ga zaman lafiya da zaman tare da juna da gwamnatin jihar ta samar.
Saboda haka, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya yi kira da a tabbatar da bin doka da oda tare da samar da daidaito a fagen siyasar jihar.
Gwamnatin ta gargadi duk wanda ya karya wannan umarni cewa za a dauki matakan da suka dace na shari’a a kansa.
Haka kuma, ta umurci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tabbatar da aiwatar da wannan umarni domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar tare da tabbatar da zaman lafiya.

No comments