Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙara tsaurara samamen da take kai wa ƙungiyoyin ta’addanci, inda ta cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa ...
Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙara tsaurara samamen da take kai wa ƙungiyoyin ta’addanci, inda ta cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar shugaban ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Dogo Giɗe, tare da wasu mutane 60 da ake zargi da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ta’addanci a wasu jihohin ƙasar.
An gudanar da kamen ne tsakanin ranakun 12 da 13 ga Agusta, yayin da dakarun soji ke gudanar da samamen da suka dogara da bayanan sirri, tare da kai farmaki kan hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda, masu taimaka musu da kuma maboyarsu. An kuma ƙwato makamai, kayan sojoji da wasu kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.
A Jihar Kaduna, dakarun Bataliya ta 4 ta Horas da Sojoji sun cafke wani mutum da ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar ISWAP a shingen binciken ababen hawa na Kadage.
An cafke mutumin ne a lokacin da ake zargin yana jigilar rigunan kamfen ɗin sojoji na ƙasashen waje guda bakwai zuwa wata maboyar ‘yan ta’adda.
A cewar sojojin, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin na cikin makusantan Dogo Gide, kuma yana taimaka masa wajen samar da kayan aiki da sauran abubuwan da ake buƙata.
Dakarun sun kwato daga hannunsa yadi 23 na kayan kamfen na ƙasashen waje, wayoyin hannu guda biyu, katunan ATM guda uku da katin shaida.
A Jihar Adamawa kuma, dakarun Bataliya ta 226, tare da haɗin gwiwar mafarauta na yankin, sun kai samame wani tashar mota da ke Gombi bayan samun bayanan sirri kan wasu mutane da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda.
Rahotannin leƙen asiri sun nuna cewa waɗanda ake zargin suna fakewa da sana’o’in ƙananan ma’aikata da masu sayar da kaya a titi.
An cafke mutane 60 yayin samamen, kuma yanzu haka hukumomin tsaro na gudanar da bincike a kansu.
A wani ɓangare kuma, rundunar soji ta ƙara faɗaɗa farmakinta a Arewa maso Yamma, inda Kwamandan Fagen Aiki na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, ya ƙaddamar da Operation Clean Sweep IV.
Sabon samamen ya haɗa hare-haren ƙasa da na sama domin tunkarar ‘yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da makamai a yankin.
Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce sabon aikin zai haɗa hare-haren ƙasa da na sama domin tunkarar barazanar da aka gano a jihohin Arewa maso Yamma.
Ya ce manufar ita ce rage ƙarfin ‘yan ta’adda, tarwatsa hanyoyin motsinsu da jigilar kayayyaki, tare da hana su kafa sansanoni a cikin al’ummomin Nijeriya.
A Jihar Katsina, dakarun soji sun gudanar da samamen share hanya a ranar 12 ga Agusta a yankunan da ake zargin ‘yan ta’adda sun kafa sansani a Ƙaramar Hukumar Dutsinma.
Danja ya ce aikin ya jefa ‘yan ta’addan cikin matsin lamba, lamarin da ya tilasta musu barin matsugunansu zuwa dazuzzukan da ke kewaye.
Ya ce aikin share yankin daga ‘yan ta’adda na ci gaba.
A Zamfara kuwa, rundunar sojin sama ta Operation Fansan Yamma ta kai hare-haren sama masu inganci kan wasu ‘yan ta’adda da aka ce sun taru a kan babura a Ƙaramar Hukumar Anka.
Sojojin sun ce hare-haren sun kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da waɗanda suka tsira suka tsere zuwa dazuzzukan da ke kusa.
A wani samame na daban, dakarun Brigade ta 1 sun gano wani bam mai linzami kirar RPG yayin sintiri a yankin Tunga-Jambako da ke Ƙaramar Hukumar Maradun, bayan wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai a baya.
A Jihar Benue, dakarun da ke ƙarƙashin Operation Whirl Stroke sun cafke wasu mutane biyar da ake zargi da kasancewa ‘yan ta’adda yayin ayyukan soji a Chito, Jootar da Ikyior, duk a Ƙaramar Hukumar Ukum.
Dakarun sun kuma lalata wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’addan ke fakewa, tare da kwato babura biyu da bindigogi ƙirar gida guda biyu.
A Jihar Borno kuwa, dakarun soji sun tare mata biyar da yara bakwai da ake zargin ‘yan uwan wasu ‘yan ta’adda ne a Ƙaramar Hukumar Mafa.
Haka kuma, an tare wasu yara maza shida a Ajiri bayan rahoton cewa sun tsere daga ƙauyen Murofari sakamakon arangama tsakanin ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu hamayya da juna.
Danja ya ce tarwatsa hanyar sadarwar ƙungiyar Lakurawa na daga cikin manyan abubuwan da Operation Clean Sweep IV ta sanya a gaba.
Ya ce aikin na da nufin hana ‘yan Lakurawa kutsawa cikin Nijeriya ko samun ƙarin mayaƙa da kayayyaki, tare da hana su amfani da yankunan kan iyaka a matsayin hanyoyin jigilar mutane da kayayyaki ko kafa sansanonin aiki.
A cewarsa, ƙaddamar da Operation Clean Sweep IV ya nuna cewa Operation Fansan Yamma na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tunkarar sabbin barazanar ta’addanci da ke tasowa a yankin.
Ya ce rundunar ta kuduri aniyar kare fararen hula, tabbatar da tsaron iyakokin Nijeriya da kuma hana ‘yan ta’adda sake haɗuwa, samun ƙarin ƙarfi ko kafa sabbin sansanonin aiki a cikin ƙasar.
.jpg)
No comments