Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Kira Da A Tabbatar Da Gudanar Da Zaɓen Jihar Osun Cikin Lumana Da Adalci

  Daga Aliyu Samba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbatar...

 


Daga Aliyu Samba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun cikin lumana da gaskiya.

Al’ummar Jihar Osun za su fito rumfunan zaɓe a gobe Asabar, 15 ga watan Agusta 2026, domin zaɓen wanda zai jagoranci jihar, inda ‘yan takara 15 ke neman kujerar gwamnan.

Daga cikin ‘yan takarar akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, na jam’iyyar PDP, da ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da kuma ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Honarabul Najeem Salaam.

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci masu zaɓe a jihar da su fito su gudanar da hakkinsu na ɗan ƙasa cikin lumana, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen.

Ya ce INEC na da alhakin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin tsari, gaskiya, ’yanci da adalci, yana mai buƙatar hukumar ta tabbatar da amincin tsarin zaɓen.

Shugaban Ƙasar ya ce zaɓen Osun shi ne na ƙarshe cikin zaɓukan da ake gudanarwa ba tare da haɗa su da sauran zaɓuka ba kafin babban zaɓen 2027, don haka ya kamata INEC ta yi amfani da shi wajen nuna wa ’yan Najeriya shirinta na gudanar da zaɓuka masu inganci.

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya da shugabannin sauran hukumomin tsaro da ke cikin aikin zaɓen da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe domin hana masu tayar da hankali kawo cikas ga tsarin.

Ya jaddada cewa dole ne a kare jami’an zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a domin su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko barazana ba.

Shugaban Ƙasar ya kuma ƙarfafa gwiwar masu zaɓe da su fito da yawa domin zaɓar ɗan takarar da suke so, yana mai cewa an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana, ’yanci da adalci.

Shugaba Tinubu ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Osun dole ne ya kasance abin da ya bayyana ra’ayin al’ummar jihar.

No comments