Daga Aliyu Samba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Tattalin Arziƙin Tashoshin Jiragen Ruwa ta Njjeriy...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Tattalin Arziƙin Tashoshin Jiragen Ruwa ta Njjeriya (NPERA) ta shekarar 2026, matakin da ya bai wa Majalisar Kula da Masu Safarar Kaya ta Nijeriya (NSC) cikakken ƙarfin doka wajen gudanar da ayyukan sa ido da daidaita harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa.
Babban Sakataren NSC, Dakta Pius Akutah, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tantance, inda ya gode wa Shugaba Tinubu bisa sanya hannu kan dokar.
Masana harkokin ruwa sun ce dokar ta buɗe sabon babi wajen samar da cikakken mai kula da harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa, wanda zai samu ikon ɗaukar mataki kan masu gudanar da ayyukan tashoshin da suka karya ƙa’idoji.
Masanin harkokin ruwa, Dakta Eugene Nweke, ya ce dokar ta kasance sakamakon ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi tun bayan bai wa kamfanoni damar gudanar da tashoshin jiragen ruwan Najeriya a shekarar 2006.
Ya ce a shekarar 2014 Gwamnatin Tarayya ta bai wa NSC matsayin mai kula da harkokin tattalin arziƙin tashoshin jiragen ruwa na wucin gadi, yayin da ake jiran samar da cikakkiyar dokar da za ta ba da wannan iko.
A cewarsa, kafin sanya hannu kan sabuwar dokar, NSC na gudanar da wasu ayyukan sa ido bisa manufofin gwamnati da kuma wata sanarwar gwamnati ta shekarar 2015.
Ya ce sabuwar dokar ta bai wa hukumar da za ta gudanar da aikin ikon kula da kuɗaɗen fito da kaya, farashi da caji, gasa tsakanin masu samar da ayyuka da kuma bayar da lasisin gudanar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa.
Dokar ta kuma tanadi hanyoyin warware takaddamar kasuwanci da ka iya tasowa a harkokin tashoshin jiragen ruwa.

No comments