Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Alhaji Indimi Ya Ƙi Amincewa Da Hukuncin Bai Wa 'Ya'yansa Dala Miliyan 43 Da Kotu Ta Yanke

Hamshaƙin attajirin Nijeriya kuma wanda ya kafa kamfanin Oriental Energy Resources, Alhaji Muhammadu Indimi, ya nemi izinin shiga cikin ƙara...


Hamshaƙin attajirin Nijeriya kuma wanda ya kafa kamfanin Oriental Energy Resources, Alhaji Muhammadu Indimi, ya nemi izinin shiga cikin ƙarar ɗaukaka ƙara da aka shigar kan hukuncin kotu da ya umarci kamfanin ya biya tagwayen ’ya’yansa mata, Zara da Ameena Indimi, dala miliyan 43.51.

Matakin na zuwa ne bayan sabon salo da shari’ar ta ɗauka, wadda ta ja hankalin masana doka da masu sharhi kan batutuwan haƙƙin masu hannun jari da kuma gadon kamfanonin iyali masu zaman kansu a nahiyar Afirka.

Indimi ya gabatar da buƙatar ne domin ya shiga shari’ar da kansa, duk da cewa kamfanin Oriental Energy ya riga ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a watan Fabrairu.

A hukuncin nata, kotun ta bai wa Zara da Ameena nasara bayan sun yi ƙorafin cewa an hana su ribar hannayen jarin da ya kamata su samu, bayan an rage kaso na hannun jarinsu a kamfanin.

Shari’ar ta wuce rikicin cikin gida, inda ta zama muhimmin ƙalubale na shari’a kan mallakar hannayen jari a ɗaya daga cikin manyan kamfanonin mai na ’yan asalin Najeriya, tare da jawo muhawara kan yadda ake tafiyar da kamfanoni masu zaman kansu.

Takardun kotu sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga batun hannayen jarin Zara da Ameena a Oriental Energy Resources.

’Yan’uwan sun bayyana cewa tun farko kowacce daga cikinsu tana da kusan kashi biyar cikin ɗari (5%) na hannun jarin kamfanin, amma daga baya aka rage shi zuwa kusan kashi 0.63 cikin ɗari. A cewarsu, hakan ya sa ribar da suke samu ta ragu matuƙa bayan kamfanin ya ayyana rabon riba na dala miliyan 435.1 a shekarar 2016.

A watan Fabrairu, Babbar Kotun Tarayya ta amince da hujjojin ’yan’uwan, inda ta yanke cewa har yanzu suna da haƙƙin samun riba bisa ga tsohon kaso na hannun jarinsu, tare da umartar Oriental Energy ya biya su dala miliyan 43.51.

Sai dai kamfanin ya ɗaukaka ƙara, yana mai cewa rage hannayen jarin da aka yi wa Zara da Ameena ya kasance bisa doka, an yi canjin ne da yardarsu, kuma an riga an sasanta batun ta hanyar wasu yarjejeniyoyin kuɗi da aka cimma a baya.

Yanzu haka ana sa ran Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta fara yanke hukunci kan ko Muhammadu Indimi zai shiga shari’ar a matsayin ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki, kafin ta fara sauraron ainihin ƙarar.

Muhammadu Indimi ya kafa kamfanin Oriental Energy Resources a farkon shekarun 1990, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan kasuwar mai na farko da suka mallaki manyan kamfanonin mai na ’yan asalin Najeriya.

A tsawon shekaru, kamfanin ya bunƙasa ya zama ɗaya daga cikin manyan kamfanonin hakar ɗanyen mai masu zaman kansu a ƙasar, inda yake da hannun jari a manyan rijiyoyin mai da ke cikin teku, ciki har da Ebok, Okwok da kuma OML 115.

Har ila yau, Oriental Energy ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan kamfanonin ’yan asalin Najeriya da ke shiga harkar bincike da haƙo ɗanyen mai, bayan sauye-sauyen manufofi da aka aiwatar domin ƙarfafa mallakar kadarorin mai da hannun ’yan ƙasa.

No comments