Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NASARAWA: Sanata Onawo Ya Koma Jam’iyyar APM, Ya Bayyana Aniyar Tsayawa Takarar Gwamna

Daga Zubairu Lawal, Lafia Sanata Mohammed Onawo, mai wakiltar Mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam’i...

Daga Zubairu Lawal, Lafia

Sanata Mohammed Onawo, mai wakiltar Mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), domin neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa.

Sanatan, wanda aka zabe shi a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 2023, ya fice daga PDP sakamakon rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar, inda daga bisani ya koma ADC. Sai dai ya sake ficewa daga ADC bayan zaben fidda gwani na takarar gwamna, wanda ya ce an yi magudi a cikinsa.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Lafia, Onawo ya ce ya yanke shawarar ficewa daga ADC ne bayan gudanar da shawarwari masu yawa da al’ummar mazabarsa, dattawan jihar, abokan siyasarsa da sauran manyan masu ruwa da tsaki a fadin Jihar Nasarawa.

A cewarsa, matakin ya samo asali ne daga bukatar samun sabon dandali na siyasa wanda ya dace da manufofinsa na shugabanci mai bai wa kowa dama, ci gaban al’umma daga tushe da kuma tabbatar da hadin kai a Jihar Nasarawa.

Sanatan ya bayyana zaben fidda gwani na takarar gwamna da jam’iyyar ADC ta gudanar a Jihar Nasarawa a matsayin abin kunya, yana mai cewa ya fi ma abin da ya sa suka bar jam’iyyar PDP muni.

Ya ce, “Ni ba ƙwararre ba ne wajen binciken rubuce-rubuce, amma idan aka duba sakamakon zaben da ido, za a iya ganin cewa mutum guda ne ya rubuta ɗaukacin sakamakon. Kuma ba a yi wani yunƙuri na gaskiya domin ganin an magance matsalar ba. Don haka na fahimci cewa wannan ba gida ba ne da ya kamata in ci gaba da zama a cikinsa.

“Na kasance a shirye na amince da sakamakon zaben, na ci gaba da zama tare da jam’iyyar tare da yi mata aiki, da ace an samar da filin takara mai adalci ga dukkanmu da muka shiga zaben. Amma an yi magudi a sakamakon cikin rashin tsoro.

“Na yi wa al’ummarmu hidima cikin ƙwazo a Majalisar Dattawa, kuma na yi imanin cewa lokaci ya yi da za a ɗaukaka wannan hidima zuwa wani matsayi mafi girma.

“Bayan gudanar da shawarwarin da suka dace, na yanke shawarar shiga jam’iyyar APM tare da amsa kiran da aka yi mini na tsayawa takarar gwamnan Jihar Nasarawa a shekarar 2027.”

Ya bayyana cewa jihar na buƙatar shugaban da ya fahimci bambance-bambancen al’ummarta kuma zai iya haɗa kan dukkan ƙabilu da mabiya addinai.

Onawo ya ce yana da gogewar siyasa, ƙwarewa a fannin aikin majalisa da kuma ingantaccen tsari na siyasa tun daga tushe, musamman a Yankin Sanatan Nasarawa ta Kudu. Ya ƙara da cewa shi ne zabin da ya dace kuma sahihi ga al’ummar jihar a shekarar 2027.

“Na taba zama ɗan Majalisar Wakilai na tsawon wa’adi biyu, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, sannan yanzu ina matsayin Sanata. Na gina kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa a faɗin jihar da ma wajenta. Saboda haka, da yardar Allah, ni ne zan zama gwamna na gaba na Jihar Nasarawa,” in ji shi.

Ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai mayar da hankali kan al’umma tare da tabbatar da wadata ga kowane gida, bisa la’akari da ayyukan da ya gudanar a baya da kuma waɗanda yake yi a halin yanzu.

Onawo ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar APM za ta lashe zaben gwamnan Jihar Nasarawa, matukar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da zabe cikin ‘yanci, adalci da sahihanci a shekarar 2027.

No comments