Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA ƊUMI-ƊUMI: Yadda Aka Kama Masu Gudanar Da Cibiyar Lafiya Ta Bogi A Kano

Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane da ake zargin suna gudanar da wata cibiyar lafiya ba bisa ƙa'ida ba a ...




Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane da ake zargin suna gudanar da wata cibiyar lafiya ba bisa ƙa'ida ba a unguwar Panshekara da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, bayan sun yaudari jama'a da sunan bayar da magani kyauta.

An gudanar da samamen ne haɗin gwiwar Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu (PHIMA), Cibiyar Dakile da Yaƙi da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) da kuma Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Rundunar Jihar Kano, a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na kare lafiyar al'umma.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da mazauna yankin suka kai wa gwamnati kan yadda ake gudanar da aikin ba tare da izini ba.

Ya ce da zarar an samu rahoton, aka tura tawagar jami'an Ma'aikatar Lafiya, PHIMA da KNCDC zuwa wurin, inda suka kama waɗanda ake zargin, kafin daga bisani a miƙa su ga Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano.

A cewarsa, a halin yanzu ana tsare da waɗanda ake zargin a Hedikwatar Rundunar 'Yan Sanda da ke Bompai domin ci gaba da bincike.

Dakta Yusuf ya bayyana cewa mutanen suna gudanar da ayyukansu ne ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna Brother Paul Legacy Foundation, wadda suka bayyana a matsayin ƙungiya mai zaman kanta (NGO), inda suke rarraba katunan rajista masu ɗauke da sunan ƙungiyar tare da karɓar kuɗi daga jama'a da sunan ba su magani.

Ya ƙara da cewa binciken farko da jami'an Ma'aikatar Lafiya, PHIMA da KNCDC suka gudanar ya tabbatar da cewa jagoran ƙungiyar da sauran waɗanda ake zargin ba ƙwararrun ma'aikatan lafiya ba ne, kuma ba su da wata takardar shaidar da ta tabbatar da cancantarsu a fannin kiwon lafiya.

Kwamishinan ya ce katunan rajistar da suke rabawa, waɗanda ke ɗauke da adireshi a Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, sun yi alƙawarin bayar da "magani kyauta", domin jawo hankalin mutane su faɗa tarkonsu.

Dakta Yusuf ya yi kira ga al'ummar Kano da su guji neman magani wajen mutanen da ba su da lasisi ko kuma masu ikirarin ba da magani ba tare da izini ba, yana mai jaddada cewa ya kamata a riƙa neman kulawar lafiya ne kawai a cibiyoyin lafiya da gwamnati ta amince da su da kuma wajen ƙwararrun ma'aikatan lafiya masu lasisi.

Ya kuma yabawa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Rundunar Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Bakori, bisa yadda ta gaggauta ɗaukar mataki kan lamarin.

Haka nan, ya jinjinawa mutanen da suka kai rahoton, yana mai cewa hakan ya nuna muhimmiyar rawar da jama'a ke takawa wajen kare lafiyar al'umma.

A ƙarshe, Kwamishinan ya buƙaci al'umma su ci gaba da kai rahoton duk wani abu da suka yi zargin ya shafi ayyukan lafiya ba bisa ƙa'ida ba ga hukumomin da suka dace, yana mai tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da yaƙi da masu yin bogi a fannin lafiya domin kare rayuka da tabbatar da cewa ana gudanar da ayyukan lafiya cikin ƙwarewa da bin doka.

No comments